Cutar coronavirus da yake yaduwa a duniya kamar wutar daji musamman a ‘yan kwanakinnan ya bayyana a Najeriya.
Ma’aikatar Lafiya ta kasa ta bayyana cewa wani dan kasar Italy ya shigo Najeriya da cutar #coronavirus daga kasar Italy.
Ma’aikatar ta bayyana cewa, wannan mutum dai ya shigo Najeriya ne daga kasar Italy.
Bayan kwana daya da shigowa sai rashin lafiya ya bayyana a jikin sa.
Daga nan sai aka kai shi asibiti inda aka gano cewa ya na dauke da cutar.
Gwamnati tace wannan bawan Allah na kwance a asibiti a Legas ana duba shi.