An tsige Shugaban Masu rinjaye na Majalisar Dokokin Jihar Kano, Lawan Madari.
Tsige shi ya biyo bayan wani muradi ne da Danmajalisa Mai wakiltar Karamar Hukumar Bunkure, Uba Gurjiya ya nemi a tsige shi, kuma wakilan APC 23 daga cikin 28 suka amince.
An maye gurbin sa da Honorabul Kabiru Dashi, bayan Dan Majalisa Mai Wakiltar Karamar Hukumar Sumaila, Hamza Masu ya bada muradin a nada shi sabon Shugaban Masu Rinjaye.
Uba Gurjiya wanda ya yi sanadiyyar tsige Shugaban Masu Rinjaye dai sabon-shigar Majalisa ne. A ranar Talata Kakakin Majalisa, Abdulaziz Gafasa ya rantsar da shi, bayan ya yi nasara a zaben-da-bai-kammalu ba da aka gudanar makonnin da suka gabata.
Majalisar Jihar Kano ta sha fama da tsige-tsige tun bayan zaben 2015. An tsige Kakakin Majalisa sau uku.
Idan ba a manta ba an yi sa-in-sa da Lawal Madari a ranar Talata, inda ya nuna rashin amincewa a nada wani Sakataren ilmi na Karamar Hukuma.
Masu yin fashin baki sun ayyana cewa hakan na da nasaba da yadda Honorabul Madari ya kafe cewa bai yarda a nada wani shugaban hukuma ba . Akwai yiwuwar a dalilin haka, majalisar ta tsige shi saboda yayi jayayya da yadda gwamnati ke so wanda ita ce aiko da sunan shugaban hukumar majalisa.