Hukumar kula da kiyaye abinci ta kasa FCCPC ta kama abinci da aka shigo dasu daga kasar Chana da kwanakin aikin su ya kare.
Hukumar FCCPC ta bayyana cewa ta kama nama dabam-dabam da kwanakin aikin su ya kara a babban shagon ‘Panda’ dake Abuja.
Panda babbar kanti ne da ‘yan kasar Chana suke siye da siyar wa a ciki musamman kayan abinci, sannan ba su bari ma ‘yan Najeriya su shiga duk da yana Abuja ne.
Shugaban hukumar Babatunde Irukare ya ce a dalilin haka hukumar ta rufe wani sashen katafaren kanti har sai an kammala bincike akai.
Irukare yace namun da aka samu a wannan kanti sun hada da macizai, kifi, kwadi da dai sauran su sannan da dama daga cikinsu kwanakin aikin sun kare.
Ya ce hukumar ta samu labarin cewa akwai wani bangare a shagon da ake boye wasu kayan abinci wanda ake hana mutane musamman ‘yan Najeriya shiga wannan sashe.
“Mun aika da wasu ma’aikatan mu a boye wanda suke je suka tabbatar mana da zaman wannan wuri sannan da kayan dake cikin wurin.
Ya kuma ce hukumar za ta sanar wa hukumar kwastam da bangaren kiwon lafiya na tsashoshin jiragen saman kasar nan da su kara sa ido domin hana shigowa da kayan abincin da ka iya hadassa cututtuka a kasar nan musamman wadanda ake shigowa da su daga kasar Chana.
Sai dai wani manajan kantin ya musanta haka yana mai cewa hukumar FCCPC bata rufe kowani sashen a kantin ba.