Bayan daukar tsawon watanni ana binciken harkallar cuwa-cuwar da aka zargin ya tafka, a karshe dai Shugaba Muhammadu Buhari ya dakatar da Modibbo Kawu, Shugaban Hukumar Kula da Gidajen Radio da Talbijin ta Kasa (NBC).
An dakatar da shi, watanni masu yawa bayan Hukumar ICPC ta sharwarci a dakatar da shi tun da dadewa.
A lokacin, ICPC ta bayar da shawarar a dakatar da Modibbo, tare wasu masu mukaman gwamnati su 32, bisa zargin su da ake yi da harkalla, kuma ana tuhumar su a kotu.
Majiya a ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da cewa an damka wa Kawu takardar dakatarwa a ranar Alhamis, inda aka dakatar da shi daga zuwa aiki, har sai yadda ta kaya bayan kammala bincike.
Wata majiya kuma ta tabbatar da cewa an damka wa Armstrong Idachaba wasikar kasancewa Shugaban Riko. Idachaba shi ne daraktan Sa-ido da Bibiyar Shirye-shiryen da Tashoshin Radiyo da Talbijin na kasar nan ke watsawa.
Akwai kuma wata majiya a hedikwatar ICPC da ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa an dakatar da Kawu har sai an kammala shari’ar da aka maka shi kotu tukunna.
Za a iya maida shi a kan kujerar sa, matsawar kotu ba ta kama shi da laifin komai ba.
Kokarin a samu jin ta bakin Kawu ya ci tura, domin an kira shi bai dauka ba. Kuma an tura masa sakon neman tabbatar da gaskiyar magana, amma bai dauka ba.
Daga nan kuma duk sauran wadanda aka tambaya a ofishin NBC da na Sakataren Gwamnatin Tarayya, sun shaida cewa ba su ma ji labarin dakatarwar ba.
An gurfanar da Kawu shi da wasu mutum biyu, a kotu, ranar 2 Ga Mayu, 2019, a kan zargin su da duma hannaye cikin naira bilyan 2.5.
Ana zargi da tuhumar su da laifin hada baki su karkatar naira bilyan 2.5n su da haka baki wajen karkatar da kudaden
Wannan zargi dai sai da ta kai an jajibo wa Ministan Yada Labarai, Lai Mohammed cikin harkalla, wanda shi ne ya amince Kawu ya bayar da kwangila ta naira bilyan 2.5 ga kamfanin Pinnacle Communications Ltd.
Discussion about this post