Dalilin cire Farida Waziri daga shugabancin EFCC -Jonathan

0

Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan, karyata dalilan da Farida Waziri na cire ta da ya yi daga Shugabancin Hukumar EFCC a cikin 2011.

Farida ta bayyana cewa Jonathan ya cire ta saboda ta kama hanyar binciken wasu gaggan masu harkallar mai a kasar nan, wadanda ke da daurin gindin Jonathan.

Ta kara da cewa wani karin dalilin cire ta shi ne saboda ta ki kamfatar kudade ta taimaka wa tafiyar kamfen din Jonathan a zaben 2011.

Farida ta yi wadannan ikirari a cikin wani littafin ta da zai fito kwanan nan, mai suna ‘Farida Waziri: One Step Ahead.

A cikin littafin Farida wadda gagaggar ma’aikaciyar dan sanda ce, ta yi bayanin yadda aka kulla sharrin yunkurin juyin mulki ha gwamnatin marigayi Abacha, abin da ta ce duk sharri ne kawai da tuggu.

Sai dai kuma buga tsakuren abin da littafin ya kunsa ke da wuya, sai Jonathan ya fito ya karyata ta.

Cikin wata sanarwa da Kakakin Yada Labarai na Jonathan mai suna Ikechukwu Eze ya fitar, ya ce an cire Farida ne saboda wasu dalilai na sirri, wadanda sirrin gwamnati ne, kuma babu bukatar a fallasa shi a yanzu.

Daga nan ya ja hankalin ta cewa ta daina daukar aikin gwamnati kamar aikin gado, wanda mutum ba zai taba bari ba.

“Ban kullaci Farida ba, kuma ba ni da wata nifaka da ita. Dalilan da ta fada ba gaskiya ba ne. Amma ya kamata a sani idan mai rike da wani mukami ya aikata abin da zai iya shafar alkiblar Najeriya a kasashen ketare da cikin gida, to don an cire shi ba wani abin hakilo da tayar da jijiyoyin wuya ba ne.

Share.

game da Author