Sanata Ibrahim Geidam, tsohon gwamnan Jihar Yobe, kuma wanda ya nemi gabatar da kudirin kafa hukumar kula da jin dadin tubabbun Boko Haram, ya bayyana dalilin sa.
An dai rika ragargazar sa a ciki da wajen majalisa, ana cewa wannan gurguwar shawara ce kuma mai hadarin gaske.
Sanatoci da dama sun ki amincewa da kudirin, wadanda suka ce asarar kudi ce, kuma maida hannun agogo baya ne.
Wasu kuma sun ce ai kamata ya yi a kashe kudin wajen sake gina wuraren da Boko Haram suka lalata da kuma daukar dawainiyar kulawa da jikkatattun sojojin da Boko Haram suka illata.
Dalilan Sanata Geidam
Sanatan ya ce idan aka kafa hukumar, za ta taimaka wa tubabbun Boko Haram su sake shiga cikin al’umma, su shiga siyasa, su koma turbar addini a cikin jama’a.
Geidam ya ce hakan zai kara kawo hadin kai fa yafe wa juna, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito ya furta a wani taron manema labarai da ya kira a Abuja, a ranar Talata.
Ya ce hakan zai sa wadanda ke cikin Boko Haram idan suka ga yadda aka karbi tubabbun, su ma su ajiye makaman su su tuba.
Sannan kuma ya je gwamnati za ta iya amfani da wadanda suka tuba din domin su yi yaki da kangararun da suka ki ajiye makamai.
“Hukumar za ta taimake su wajen yaye musu mummunar akidar da ta dakushe musu kwakwalwa da tunani.
“Idan tubabbu suka dawo cikin jama’a suka zauna, za su rika bayar da labarin illar da mummunar akidar Boko Haram ta yi musu, daga nan matasa da dama za su guji fadawa cikin tarkon Boko Haram.
Tsohon Sanata Shehu Sani ya ce babu wata bukatar kafa hukumar, domin akwai hukumar kula da yankin Arewa maso Gabas da aka kafa a zamanin mulkin majalisar dattawa na karkashin Sanata Bukola Saraki.