Dalilai 5 da ya sa Rahama Sadau ce babbar aminiyata a Kannywood – Sadiq Sani Sadiq

0

Fitaccen jarumin Kannywood, Sadiq Sani Sadiq ya bayyana cewa a duk fadin farfajiyar Kannywood ba shi da wanda tafi kwanta masa a rai kaman jaruma Rahama Sadau.

Sadiq ya fadi haka ne da yake hira da BBC HAUSA a Abuja.

Sadiq ya ce bashi da budurwa a Kannywood sai dai yana da aminiya babba a farfajiyar wanda ya saba da ita kuma akwai mutunci da alkawari da yadda a tsakanin su sosai.

Sadiq ya wasa Rahama Sadau matukar wasawa sannan ya kara da cewa ‘irin su kadan ake samu a tsakanin mutane.’

1 – Rahama Sadau ta san kima da darajar mutum. Muddun kuka shaku da ita zaka san haka.

2 – Rahama Sadau na da rikon amana, muddun ka amince mata, tabbas ba za ta baka kunya ba.

3 – Rahama Sadau na da Alkawari, idan ta dauki alkawari ina tabbatar maka ba zata saba ba. Zata yi kokarin ganin ta cika wannan alkawari.

4 – Rahama na da adana sirrin mutum. Muddun ka gaya mata wani abu naka na sirri, ‘toh kaje kayi barcin ka har da minshari, domin babu inda zaka ji shi.’

5 – Tana da gaskiya a dukka al’amurorinta. Tana da amana da sanin ya kamata.

A karshen hirar sa da BBC Hausa, Sadiq ya jinjina wa wasu daga cikin jaruman farfajiyar Kannywood da suke tare dashi sannan yayi aiki dasu  kamarsu Bello Mohammed Bello, wanda shine sanadiyyar fadawar sa harkar fim, Sai Ali Nuhu da ya yi masa masauki a Kano a lokacin da ya zo da Jos, sai Aminu Saira da Adam Zango.

Share.

game da Author