‘Yan Najeriya na ci gaba da bayyana ra’ayoyin su dangane da matsalar tsaro, inda a wata kuri’ar jin ra’ayi da PREMIUM TIMES ta bayar da fili a ka Kasa, suka nemi Shugaba Muhammadu Buhari ya sallami Shugabannin Tsaro, na Tsaro, Sojoji, Sojojin Sojojin Sama da Sojojin Ruwa.
PREMIUM TIMES ta shirya jin ra’ayin a shafin ta na intranet, ta yadda sau daya kadai za a iya kada kuri’a.
Mutane 4,380 ne suka jefa kuri’ar “e” ko “a’a”. An tambayi, ” Shin ka goyi bayan Shugaba Muhammadu Buhari ya sallami Hafsoshin Tsaro?
Daga cikin mutum 4,380 da suka jefa kuri’a, 3,771 sun nemi a sallame su, yayin da 317 suka ce a bar su.
An samu mutum 292 da suka nuna ba su da ra’ayi. Sun nuna duk yadda aka yi ba su da zabi.
Dalilan Masu Neman A Sallami Su Buratai
1. Sashe na 8 na Dokar Aikin Gwamnati ta ce kada ma’aikaci ya wuce shekaru 35 ya na aiki ba tare da an yi masa ritaya ba.
To dukkan Manyan Hafsoshin Tsaro su 4 sun zarce shekaru 35 su na aiki.
2. Doka ta ce kada ma’aikataci ya wuce shekaru 60 da haihuwa kuma ya na aiki.
Dukkan su 4 babu wanda ya kai shekara 60 a duniya. Amma sun haura shekaru 35 su na aiki.
3. Wa’adin aikin su ya kare tun a ranar 13 Ga Yuli, 2017. Buhari ya nada su a ranar 13 Ga Yuli, 2015.
4. Sashe na 4 na Dokar Aiki ya ce kada a dauki nada wanda ya shige wadannan ka’idojin wani mukami da sai wanda bai shige sharuddan shekarun ba za a nada.
5. Shekarun Babban Hafsan Tsaro, Abayomi Olonisakin 57 a duniya. Amma shekarar sa 38 ya na aikin soja.
6. Shekarar Kwamandan Askarawa, Tukur Buratai 59 a duniya. Amma ya shafe shekaru 36 ya na aikin soja.
7. Shekarar Babban Hafsan Sojojin Ruwa, Ibok-Ete Ekwe Ibas 59 da haihuwa. Amma ya shafe shekaru 36 ya na aikin soja.
8. Shekarar Babban Hafsan Sojojin Sama, Saddique Abubakar 59 da haihuwa. Amma ya shafe shekaru 40 ya na aikin soja.
9. Matsalar tsaron da ke kara tabarbarewa duk kuwa da wuce wa’adin su ne ya sa aka rika yin kiraye kirayen su sauka.
10. Bukatar a samu sabbin jinin Hafsoshin Tsaro da kuma kawo sabbin dabarun kawar da matsalar tsaro, ba a tsaya kan wadanda shugabannin yanzu ke kai ba, shi ne ya kara sa jama’a nuna bukatar sallamar su.
Discussion about this post