Kotu ta yi watsi da bukatar dakatar da Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II… Kuma kotun ta bayar da umarnin a biya shi diyyar kimanin naira 200,000 kudin fansar bata masa suna da bata masa lokaci da aka yi.
Wannan al’amari dai ya faru ne a babbar kotun tarayya da ke jihar Kano, a yau Juma’ah, a inda ta yi watsi da wani rahoton da hukumar koke-koke ta gwamnati da yaki da rashawa (PCACC) ta fitar, wanda ta bukaci a dakatar da Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II, har zuwa lokacin da za’a kammala bincike a kan wadanda ake zargi da salwantar da kudin masarauta.
Mai shari’a O. A. Eguwuatu yace, PCACC ba ta bawa Sarkin damar sauraro ba, kafin a fitar da rahoton a kan sa. Hakan kuwa yaci karo da dokar adalci.
Sarkin ya maka PCACC, gwamnan jihar Kano, da kuma kwamishinan shari’ar jihar Kano a gaban kotu. Kuma ya bukaci kotun da ta bayyana cewa rahoton da PCACC ta bayyana a ranar 6 ga watan Yuni 2019, sun ci karo da hakkin sa na sauraro, kuma sun take dokar adalci.
Sarki Sanusi ya kara da cewa, bukatar kotun dai shine tayi watsi da rahoton farkon da ke danganta shi da damfara, almundahana tare da bukatar dakatar da shi.
A yayin amsa bukatar Sarkin, kotun ta bada umarnin a biya shi diyyar N200,000, kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.
A ranar larabar da ta gabata ne babbar kotun jihar Kano karkashin jagorancin Mai shari’a Sulaiman Na-Mallam, ta hana PCACC ci gaba da bincikar Sarkin.
A binciken farko da hukumar ta fitar, ta bukaci a dakatar da Sarkin kafin kammala bincikar sa a kan zargin ne, wai akan yayi sama da fadi na kudi kimanin naira biliyan 3.5. Lauyan Sarkin, Suraj Sa’ida, ya mika bayanin sa na hana hukumar ci gaba da bincikar Sarkin.
Sai dai kuma babban Malami, limamin masallacin Juma’a dake Okene, Imam Mutadha Gusau ya bayyana farincikin sa ga wannan hukunci.
Imam Murtadha wanda ya na kan gaba wajen kira da arika girmama sarakunan mu na Arewa a kowani matsayi da muka samu kan mu ya yi sharhi game da wannan nasara da Sarki Sanusi yayi a kotu.
” Ana hangen wannan binciken a matsayin wani yunkurin bata suna da bita-da-kulli daga Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, na tozarta Sarkin haka kawai, saboda hassada, wanda da yardar Allah ba zai ci nasara ba.
” Kamar yadda dai duk kuka sani ne, bayan wulakanci iri-iri da suke nunawa Mai Martaba Sarki, Gwamna Ganduje bai tsaya a nan ba, ya kirkiri sabbin masarautu guda hudu, duk dai domin ya bakanta wa Mai Martaba Sarki rai, a Gaya, Rano, Karaye da Bichi, wadanda suka kasance wai masu darajar farko.
” Sannan kuma a tarihin jihar Kano, ba’a taba samun gwamnan da ya raba kan ‘yan Kano ba, ya tarwatsa su, kamar Ganduje.
” Ganduje ya haddasa gaba da kiyayya tsakanin masu sarauta, malaman addini, ‘yan kasuwa da dattijan jihar Kano. Kai hatta ma zuri’ar gidan Dabo bai bar su a baya ba wurin raba kawunan su, a inda yake amfani da kudi domin sayen wasu daga cikin su, don su taya shi fadan da yake yi da Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II.
” Daga karshe muna addu’ar Allah ya kawo karshen wannan irin bakin mulki na gwamna Ganduje. Ina rokon Allah ya azurta Kanawa da arewa baki daya da shugabanni na kwarai, masu kishin al’ummar su, masu kokarin hada kan al’ummar su don a zauna lafiya, ba masu raba kawunan su ba.

” Ya Allah, muna tawassali da sunayen ka tsarkaka, ka tausaya muna, ka karbi tuban mu, ka azurta mu da hakuri, juriya, jajircewa da ikon cin jarabawar ka. Ya Allah ina rokon ka taimaki Masarautar Kano, ka kubutar da ita daga makircin ‘yan siyasa, tare da dukkanin masarautun mu na arewa.
” Ya Allah, kayi muna gafara, ka shafe dukkan zunuban mu, don son mu da kaunar mu ga fiyayyen halitta, Annabin rahmah (SAW).
” Ina rokon Allah ya kyauta, ya kawo muna mafita ta alkhairi, amin.
Dan uwan ku, Imam Murtadha Muhammad Gusau, ya rubuto daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za’a iya samun sa a lambar waya kamar haka: 08038289761.