A sabuwar doka da hukumar yi wa kamfanoni rajista ta kasa ta fitar, daga ranar Litinin mai zuwa duk wani da zai ziyarci hukumar CAC sai ya tsuke ya zanzare kafin a barshi ya shiga harabar hukumar.
Darektar yada labaran hukumar, Laraba Sharibu ta bayyana cewa hukumar ta yo haka saboda yadda lauyoyi ke shifowa harabar hukumar ba tare da sun yi shigan kirki ba.
” Mun lura cewa lauyoyi kan shigo mana harabar ma’aikata ba tare da sun saka kayan arziki a jikin su ba. Sai kaga lauya ya zo ko ta zo cikin yagaggon kaya wai ko gayu ne ko kuma yanga, ko kuma matsatstse sannan da gajerun siket kamar ba kwararru ba.
” A dalilin haka hukumar ta ga ya dace ta fitar da wannan doka ga kowa da kowa domin a tsaftace hukumar.
” Ko dai ka saka kaya irin na al’ada wato jamfa da wando da hula ko kuma ka sa riga da wando sannan ka zanzare ka tsuke ka fito tsaf-tsaf in ko ba haka ba ba za a barka ka shiga harabar wannan hukuma ba.
Ta kara da cewa wadannan lauyoyi ba za ka gansu haka ba idan a harabar kotu suke. ” Za ka gansu tsaf-tsaf amma da yake ba kotu bane sai su zo mana a hargitse sanye da wasu irin kayan da basu da natsuwa a ciki.
Sannan kuma tace ko dokar hukumar ta tsara irin kaya da yadda za a rika saka su ga duk ma’aikaci da wanda zai rika hudda da hukunar ko ziyarce ta.
Discussion about this post