Kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriya, Frank Mba ya bayyana cewa zaratan dakarun rundunar sun kashe akalla mahara da ‘yan kungiyar Ansaru har 250 a dajin kuduru, dake yankin karamar hukumar Birnin Gwari, a Jihar Kaduna.
Frank ya kara da cewa dakarun ‘yan sandan sun far wa wannan daji inda suka yi wa maharan zobe sannan suka rika barin wuta ta ko ina.
” A Wannan karon maharan basu ji da dadi ba domin sai da dakarun mu suka ragargaje su da albarusai inda akalla mutane sama da 250 suka sheka lahira nan take. Sannan babu jami’in mu ko daya da ya rasa ransa a wannan hari da muka kai.
Frank ya ci gaba da cewa wasu matuka jirgi mai saukar angulu biyu sun dan samu rauni a jikin su da yanzu haka suna asibiti ana duba su.
Jami’i Mba ya ce wannan shine karo na farko da aka ragargaja mahara a wani hari irin wannan sannan ya ce rundunar za ta ci gaba da kai ire-iren wadannan hare-hare a maboyan yan ta’adda da mahara da suka addabi mutane a fadin kasar nan.