CUTAR DAJI: Najeriya na daga cikin kasashen da basu samar da kula ga masu fama da cutar – Uwargidan Gwamna

0

Uwargidan gwamnan jihar Ondo Betty Akeredolu ta koka kan yadda rashin samar da kula ga mutanen dake fama da cutar daji ko kuma sankara ke yin sanadiyyar rasa rayuka da dama a kasar nan.

Betty ta fadi haka ne a taron makon tunawa da cutar daji da aka yi a Akure.

Ta ce bincike ya nuna cewa kimiya ya kawo ci gaban da za a iya warkar da wadanda suke fama da cutar.

Sai dai hakan ba shine ke faruwa a Najeriya ba domin mutane da dama sun rasu a dalilin rashin samun kula, tsadar magani, rashin sani da sauran su.

Betty ta yi kira ga gwamnati da ta mike tsaye wajen ganin ta rika wayar da kan mutane game da cutar a kasar nan tana mai cewa yin haka e yin haka zai taimaka wajen rage yawan mutanen dake rasa rayukan su a sanadiyyar wannan cuta.

Idan ba a manta ba a watan Oktobar 2019 a taron inganta kiwon lafiya da aka yi a Abuja ne ministan kiwon lafiya Osagie Ehanire ya bayyana cewa nan ba da dadewa ba gwamnati za ta bude wani asusu domin kula da masu fama da cutar daji a kasar nan.

Ehanire ya ce gwamnati za ta kafa wannan asusu ne don taimakawa masu fama da cutar a Najeriya bayan kokawar da wata mata mai suna Serah Shimenenge dake dauke da cutar ta yi kan kaluballen da ta ke fama da su.

Ya yi kira ga mutane da su kiyaye hanyoyin dake haddasa wannan cuta da suka hada da guje wa shan giya, shan taba sannan da shakar hayakin sigari cewa yin haka zai taimaka wajen dakile yaduwar cutar.

Sannan kuma gwamnati ta dauki wasu matakan da za su taimaka wajen wayar da kan mutane game da cutar domin rage yawan mace-macen mutane a kasar nan.

Share.

game da Author