Hukumar hana yaduwar cututtuka ta kasa (NCDC) ta bayyana cewa sabuwar cuta ta bullow a jihar Benuwai inda akalla mutane 104 sun kamu da cutar zuwa yanzu sannan wasu 15 sun mutu.
Chikwe Ihekweazu ya sanar da haka a Abuja da yake hira da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ranar Asabar.
Ihekweazu ya ce hukumar ta fara gudanar da bincike domin gano ko wani irin cuta ce ta bullo a jihar.
“Gwajin da muka gudanar a jikin wadanda suka kamu da cutar ya nuna cewa ba zazzabin Lassa, Ebola ko shawara bane suke dauke da sabuwar cuta ce.
” Mun aika da ruwan da mutanen jihar ke sha zuwa ma’aikatar ruwa domin gudanar da bincike.
Ya ce bincike ya nuna cewa cutar ya fara bullowa a jihar Benuwai a ranar 29 ga watan Janairu a kauyen Oye karamar hukumar Obi.
Ihekweazu ya ce a ranar Alhamis majalisar dattawa ta yi zaton ko alamun kwayoyin cutar ‘Coronavirus’ ne ya bullo a jihar. Sai dai babu mai tabbacin ko haka ne ya faru.
Ihekweazu ya yi kira ga mutane da su ci gaba da tsaftce muhallin su tare da adana abinci domin guje wa kamuwa da cututtuka.