Akalla dala milyan 675 ne Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ke bukata cikin gaggawa, domin yin ayyukan tallafin a kasashen da ke da raunin tsarin kiwon lafiya a fadin duniya, domin gujewa daga kamuwa da cutar ‘Conornavirus’.
Babban Daraktan WHO, Tedros Ghebreyesus ne ya bayyana haka da ya ke wa duniya jawabi a ranar Laraba, a Geneva, a hedikwatar Hukumar Lafiya ta Duniya.
Ya ce cutar coronavirus ta zama annoba a duniya, wadda a daidai lokacin da ya ke jawabi ta bulla a kasashe 25 banda China.
Tedros ya ce a kasar Chana dai mutum 24, 363 sun kamu da cutar, ya zuwa lokacin da ya ke jawabi.
Ya kara da cewa kashi 99 bisa 100 na wadanda kan nuna alama, idan aka gwada su, akan tabbatar da cutar a jikin su.
“A sauran kasashe banda Chana kuwa, an samu adadin mutum 191 da suka kamu da cutar ta Coronavirus.
“Har zuwa ranar Laraba dai ba a samu sahihin rahoton bullar cutar a wata kasa ko daya cikin Afrika ba. Sai dai zargi da rahotanni marasa tabbas kawai.
Fargabar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO)
Hukumar WHO ta ce babban fargabar da ta ke yi shi ne kada wannan cuta ta kai ga shiga kasashe wadanda ba su da wani tsarin kula da lafiyar jama’a na kirki. Domin za ta yi muni sosai.
” Dalilin haka ne mu ka yi gaggawar kafa asusun nan gudumawar dala milyan 675 domin gaggata kai dauki zuwa kasashen da ba su da wani sahihi, ingantacce ko kwakwaran kiwon lafiyar al’ummar su.
“Babban abin fargaba ne cewa akwai kasashen da ko na’urar gwajin gane alamomin kamuwa da.cutar ba su ma da shi, ballantana kuma a yi maganar dabarun gaggauta tsaida kamuwa da cutar, ko kula da kuma killace wadanda suka kamu.” Inji Tedros, Shugaban WHO.
Ya ce su na bukatar tara wadannan makudan kudade daga wannan wata na Fabrairu zuwa Afrilu.
Tuni dai har Gidauniyar Bill & Melinda ta Bill Gates ta bayyana bayar da gudummawar naira milyan 100 cur.
Discussion about this post