#CORONAVIRUS: Yadda dan Italy ya tsallake siradin bincike a filin jirgin Lagos dauke da cuta

0

Yayin da ‘yan Najeriya ke cikin tunani, al’ajabi har da sallallamin yadda jami’an tsaro da na kula da lafiya suka yi sakaci har Baturen Italy ya shigo Najeriya dauke da cutar Coronavirus, Ministan Lafiya ya yi karin haske.

Minista Osagie Ehanire, ya ce babu batun sakaci ko rashin kula ko wasarere da aiki a bangaren Najeriya.

A ganawa da manema labarai a Abuja, Ehanire ya ce sai da aka yi wa Ba’Italiyen gwaji a filin jirgin Murtala Mohammed da ke Lagos, amma ba a samu cutar a jikin sa ba.

Ya ce dalilin rashin ganin cutar a jikin Baturen, shi ne saboda a lokacin da ya shigo Najeriya cutar ba ta kai ga fara nuna alamu a jikin sa ba, shi ya sa na’urar gwaji ta masa hakaito cutar a jikin sa.

Minista ya ce a lokacin da Baturen ya shigo, zai yi wuya na’ura ta iya gano ko akwai cutar a jikin sa, saboda kwatoyin sinadaran cutar ba su rigaya sun kyankyashe a cikin jikin sa ba.

Ya ce jama’a su kwantar da hankalin su, domin Baturen na can a killace, kuma magani ya karbi jikin sa.

Sannan kuma ya ce an tabbatar ya na ci.gaba da murmurewa.

Premium Times Hausa ta bugs labarin yadda wani dan kwallon Najeriya da shi ma ke bugs kwallo a Italy, Akpan Udoh ya kamu da cutar, a ranar Alhamis a Italy.

Tuni dai muhukuntan kasar masu kula da kiwon lafiya suka killace shi, inda zai shafe kwanaki 14 a killace, kamar yadda aka yi wa Baturen da aka samu dauke da cutar a Lagos.

Share.

game da Author