Tun bayan bullar cutar Coronavirus a birin Wuhan da ke Gundumar Hubei na kasar Chana, ana tunanin kusan mutum 100, 000 sun kamu a duniya, a cikin kasarashe kusan 40.
Ta baya-bayan nan da aka samu bullar ctar a cikin ta, ita ce Najeriya, wadda aka samu wani dan kasar Italy ya shigo kasar dauke da cutar.
Ya zuwa ranar Juma’ar nan, wato karshen watan Febrairu, kasashe na ci gaba da bada rahoton bulla da kuma karuwar cutar, inda abin sai kara firgita duniya gabata cutar ke yi.
IRAN: An dakatar da sallar Juma’a, bayan ma’ataikin Shugaban Karar ya kamu da cutar Coronavirus. Doma kuma a ranar Alahamis PREMIUM TIMES HAUSA ta buga rahoton cewa Mataimakin Ministan Lafiya na Iran ya kamu da cutar Coronavrus.
ITALY: Shugaban Mabiya Darikar Roman Katilika na Duniya, Paparoma Francis, ya kamu da zazzabi, wanda hakan ya sa aka soke wani taron gangamin ganawa da wasu manyan limanan Kiristoci da aka shirya zai yi.
Ba a dai bayyana musabbabin zazzabin da ya kama Paparoma ba, amma dai ya kamu ne kwana daya bayan wani taron jawabin jimamin masu kamuwa da Coronavirus wanda ya halarta.
Kasar Italy na fama da kamuwar cutar, inda ya zuwa ranar Alhamis, sama da mutum 400 aka bada labarin sun kamu, tun bayan barkewar cutar a cikin Disamba.
An dakatar da wasu wasannin kwallo, shiga cinkoson jama’a, haka kuma kasashen masu makwautaka da Italy sun a kauracewa daga kusantuwa da kan iyakar kasar.
Daga Italy ne wanda ya kai cutar Najeriya ya fito.
SAUDIYYA: Bana Babu Batun Tafiya Umra, Sai Yadda Hali Ya Yi
A kokarin kada cutar Coronavirus ta watsu cikin Makka da Madina, kasar Saudiyya ta dakatar da masu tafiya Umra daga kowace kasa a duniya.
INGILA: Yayin da wasu kasashe suka rufe makarantu, aka ce kowane dalibi ya zauna a gida, kasar Ingila ma na tunanin rufe dukkan makarantun kasar, har sai bayan makwanni takwas.Haka dai jaridar Daily Mail ta London ta ruwaito a ranar Juma’a.
NAJERIYA:
An fara atisayen gaggawa a filin jirgin Murtala Mohammed.
Jami’ai a Babban Filin Jiragen Sama na Murtala Mohammed da ke Lagos, sun bada sanarwar, an fara daukar matakan binciken kwakwaf, atisaye tare da aikin dabarun yi wa fasinjojin da suka dira a filin feshin-a-kori-Coronavirus.
Wannan bayani ya fito ne daga bakin Babbar Manajar Hukumar Kula da Zirga-zirgar Jirage ta kasa (FAAN).
Jami’ar ta ce shirin an fara shi ne gadan-gadan domin tabbatar da gano irin kyakkyawan shirin da aka yi domin gwajin gano masu dauke da alamomin cutar.
Don haka an shawarci fasinjoji, masu hada-hada da mkwautan filin jirgin cewa kada su ga ana atisaye hankalin su ya tashi, duk gwaji ne ake yi.
Coronavirus: An dauki tsauraran matakai a jami’ao’i
Bayan tabbatar da bullar cutar Coronavirus a Najeriya, tuni an tashi tsaye wajen maida hankali a kan wasu jami’o’i.
Hakan kuwa ya fito ne daga mahukuntan jami’ar da kuma mahukuntan Najeriya.
’Yan Najeriya sun wayi gari safiyar Juma’a cikin jimamin bayyanar cutar Coronavirus a Lagos, bayan wani Bature dan Italy ya shigo Najeriya da cutar daga kasar su.
An dai gwada Baturen a Babban Asibitin Lagos da ke Idi-Araba, kuma aka tabbatar ya na dauke da cutar. Daga nan aka killace shi daban.
Ba-babba-ba-yaro: Coronavirus ta kama Mataimakiyar Shugaban Iran
An bada sanarwar cewa daya daga cikin Mataimakiyar Shugaban Iran, mai suna Massoumeh Ebtekar, ta kamu da cutar Coronavirus.
Ebtekar dai ita ce mataimakiya mai lura da sha’anin mata.
Idan ba a manta ba, Ebtekar ita ce kakakin dalibai mata wadanda suka yi garkuwa da Amurkawa 52 a Iran cikin 1979. Ana ci gaba da kula da lafiyar ta a gidan ta.
Sannan kuma Babban Shugaban Kwamitin Majalisar Iran Mai Kula da Harkokin Waje da Tsaro, Mojtaba Zolnur, shi ma ya kamu.
Dama kuma tun a ranar Laraba an bada abarin kamuwar mataimakin ministan lafiya na Iran, Iraj Harirchi.
Akalla mutum 360 ne aka tabbatar da sun kamu a Iran. Tuni dai mahukuntar kasar suka bada sanarwar dakatar da gudanar da Sallar Juma’a a wasu garuruwan yankin Arewacin kasar, inda cutar ta fara.
Makwautan Iran Sun Rufe Kan Iyakokin Su
Gudun kada abinda ya ci Doma ya shiga Awai ya ci su da yaki, tuni kasashen da ke makautaka da Iran, wadanda suka hada da Haddaddiyar Daular Labarawa (UAE), Kuwait, Bahrain, Lebanon, Afghanistan, Pakistan da Estoni, duk sun bada sanarwar rufe kan iyakokin su. Ba su yarda wani ya shigar musu daga Iran ko wani ya fita zuwa Iran ba.
An kuma takaita maziyarta kaburbura da masumiyoyin manyan malaman addinin kasar na dauri.
Coronavirus: Cutar da ta yi wa duniya rubdugu, ta ci rayuka 2801
Ya zuwa safiyar Juma’a, China ta bada sanarwar mutum 78,630 suka kamu da cutar a kasar. Kuma ta kashe mutum 2747 a Chana din.
A cikin kasashen duniya 44 banda Chana, mutum 3474 suka kamu, kuma an bada rahoton mutuwar mutum 54.
Kasashen Jamus Da Italy Sun Gigice
Ranar Alhamis, PREMIUM TIMES Hausa ta bada labarain cewa Coronavirus ta barke a Jamus, 400 sun kamu a Italy.
Ma’aikatar Lafiya ta kasar Jamus ta bayyana barkewar cutar coronavirus a kasar, inda ta ce a dan kankanin lokaci mutum goma ya kamu.
Cikin sanarwar da mahukuntan kasar suka bayyana a ranar Alhamis, sun ce yanzu haka an fantsama nema da gwajin gano duk wani mai dauke da cutar, ko kuma mai alamun kamuwa da ita.
Haka dai Ministan Lafiyar Jamus, Jens Spahn ya bayyana a birnin Berlin.
Ya ce a yanzu dai ya yanke kaunar tunanin cewa wannan annoba ba za ta tsallake kasar Jamus ba.
A Gundumar North-Rhine Westphalia an samu wasu mutum biyar sun kamu, kuma yanzu haka jami’an lafiya sun bazama nema da binciken ko akwai sauran wadanda suka kamu din.
Tuni dai wasu mutane kimanin 300 da aka tabbatar sun halarci wani bukin kalankuwa a kan iyakar Jamus da Netherland aka umarta su kai kan su ga jami’an lafiya domin a yi musu gwajin gaggawa.
Can kuma a yankin Baden-Wuerremberg, aka killace wasu mutum hudu da suka kamu, gudun kada wasu su sake kamuwa daga gare su.
A yankin Koblenz kuma, mahukuntar sojan kasar na can na fama da bincike da gwajin sojoji, sakamakon samun wani soja ya kamu da cutar a yankin.
Ita ma kasar Denmark ta bada sanarwar kamuwar wani mutum daya, bayan ya je bulaguron yawon wasan gudu cikin dusar kankara a yankin Aerwacin kasar Italy.
Tun dai a kasar Italy aka tabbatar da cewa sama da mutum 400 suka kamu.
Fargaba a Italy ta kai a yanzu wasu wasannin za a rika yin sub a tare da ’yan kallo sun shiga fili ba, gudun kamuwa da cutar.
Discussion about this post