CORONAVIRUS: WHO ta horas da mutane 25,000 kan hanyoyin dakile cutar

0

Kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta bayyana cewa akalla mutane 25,000 ne suka samun horo kan hanyoyin dakile yaduwar cutar Coronavirus a shafin da ta bude a yanar gizo.

WHO ta bude wannan shafi a yanar gizo tun a shekarar 2018 domin wayar da kan mutane musamman ma’aikatan kiwon lafiya game da cututtuka da matakan da ya kamata a bi wajen dakile yaduwar su.

Kungiyar kiwon lafiyar ta fara horas da mutane ne a ranar 26 ga watan Janairu 2020 kafin ta sanar cewa coronavirus ta zama annoba a duniya.

Adadin yawan mutanen dake samun horo kan cutar coronavirus ya karu daga 25,000 zuwa 30000 inda a kulum rana ake samun yawan mutanen dake shiga yanar gizo domin samun bayanai game da cutar.

Kungiyar ta kuma ce yawan mutanen ya karu ne bayan ta sanar cewa ta ware dala miliyan 675 domin ganin an dakile yaduwar cutar musamman a kasashen da basu da karfin yin haka.

Za a samu wannan shafi ne a OpenWHO.org. sannan duk mai ra’ayin samun bayanai game da cutar coronavirus da sauran cututtuka zai iya samu a wannan shafi.

WHO ta fasara bayanan cututtuka musamman coronavirus a harsunan da WHO ke aiki da su a duniya.

Manajan wannan shafi Heini Utunen ya bayyana cewa WHO ta fi bada karfi ne wajen samar da bayanai game da cututtuka da hanyoyin dakile su tare da fassara su a harsunan da mutane za su fi iya gane wa guda 21.

Ya ce ziyartar wannan shafi zai taimaka wajen karfafa matakan hana yaduwar cututtuka a duniya.

Share.

game da Author