Coronavirus ta kama Ministan Lafiyar Iran

0

Iran ta tabbatar da cewa wani gwaji da aka yi wa Karamin Ministan Lafiya Iran Harirchi ya kamu da cutar Coronavirus.

Wannan cuta dai ta fara bulla ne a birnin Wuhan, da ke Tsibirin Hubei na China, kuma zuwa yanzu ta watsu a cikin kasashe 30.

Tun bayan bullar ta a Iran, an bayyana cewa mutane 15 sun mutu.

Mataimakin Ministan Lafiya wanda ya kamu, shi ne ke jagorancin gaganiyar kokarin dakile ci gaba da kamuwa da cutar a Iran.

A cikin wani bidiyo da ya fitar a ranar Talata, Harirchi ya ce shi ma ya kamu da cutar, kuma an kebe shi, sannan kuma ya na ci gaba da karbar magani.

“Ni dai kawai na ji zazzabi ya rufe ni a cikin dare, sannan da aka yi min gwaji can tsakiyar dare, sai aka gano na kamu da Coronavirus.
To amma dai yanzu na killace kai na, kuma ina shan magani.

“Ina kara karfafa mana guiwa cewa nan da makonni kadan za mu shawo kan wannan cuta.” Inji ministan.

An dai ga Harirchi ya na ta murzar idanu a lokacin da ya ke wa manema labarai jawabi, inda ya ke karyata wasu rahotannin da aka ce cutar na kara bazuwa sosai.

An da nan kuma sai aka tsinkayi ya na ta tari ga kuma gumi ya karyo masa, yayi sharkaf, a lokacin da ya key i wa manema labarai jawabi.

Iran dai ta bada bayanin cewa mutane 95 ne suka kamu, amma kuma ana ganin kamar rufa-rufa ce gwamnatin kasar keyi.

Ana zargin cewa mutanen da suka kamu, sun wuce adadin 95 nesa ba kusa ba.

Ahmad Amirabadi-Farahani, yayi ikirarin cewa “Coronavirus ta bulla a birnin Qum makonni uku da suka gabata, kuma har ta kashe mutum 50 a garin.”

Hukumar Lafiya ta Majlisar Dinkin Duniya ta nuna damuwa ganin yadda Coronavirus ke yaduwa a Iran, Koriya ta Kudu da kuma Italy.

An kuma samu karin wadanda suka kamu a Hong Kong, Macao da Taiwan, ya zuwa mutum 121

Share.

game da Author