Ma’aikatar Lafiya ta kasar Jamus ta bayyana barkewar cutar coronavirus a kasar, inda ta ce a dan kankanin lokaci mutum goma ya kamu.
Cikin sanarwar da mahukuntan kasar suka bayyana a ranar Alhamis, sun ce yanzu haka an fantsama nema da gwajin gano duk wani mai dauke da cutar, ko kuma mai alamun kamuwa da ita.
Haka dai Ministan Lafiyar Jamus, Jens Spahn ya bayyana a birnin Berlin.
Ya ce a yanzu dai ya yanke kaunar tunanin cewa wannan annoba ba za ta tsallake kasar Jamus ba.
A Gundumar North-Rhine Westphalia an samu wasu mutum biyar sun kamu, kuma yanzu haka jami’an lafiya sun bazama nema da binciken ko akwai sauran wadanda suka kamu din.
Tuni dai wasu mutane kimanin 300 da aka tabbatar sun halarci wani bukin kalankuwa a kan iyakar Jamus da Netherland aka umarta su kai kan su ga jami’an lafiya domin a yi musu gwajin gaggawa.
Can kuma a yankin Baden-Wuerremberg, aka killace wasu mutum hudu da suka kamu, gudun kada wasu su sake kamuwa daga gare su.
A yankin Koblenz kuma, mahukuntar sojan kasar na can na fama da bincike da gwajin sojoji, sakamakon samun wani soja ya kamu da cutar a yankin.
Ita ma kasar Denmark ta bada sanarwar kamuwar wani mutum daya, bayan ya je bulaguron yawon wasan gudu cikin dusar kankara a yankin Aerwacin kasar Italy.
Tun dai a kasar Italy aka tabbatar da cewa sama da mutum 400 suka kamu.
Fargaba a Italy ta kai a yanzu wasu wasannin za a rika yin sub a tare da ’yan kallo sun shiga fili ba, gudun kamuwa da cutar.
Discussion about this post