CORONAVIRUS: Matakan da suka kamata gwamnatin Buhari ta gaggauta dauka -Atiku

0

Tsohon Maitaimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya ce tilas sai gwamnatin Najeriya ta tashi haikan wajen kokarin dakile bullar cutar Coronavirus, maimakon a tsaya ana dawurwurar neman wanda za a dora wa laifi.

Atiku ya ce ta haka ne kawai Najeriya za ta iya shawo kan Coronavirus a cikin gaggawa. Ya kara da cewa ya na da tabbacin Najeriya za ta ci galaba a wannan karo ma, kamar yadda cikin 2014 aka dakile bullar cutar Ebola a Najeriya.

Najeriya ta wayi garin ranar Juma’a da labarin bullar cutar Coronavirus a Lagos, bayan da wani Baturen Italy mai dauke da cutar ya shigo Lagos da nufin kasuwanci.

Wannan cuta dai ta kashe dubban mutane a duniya, musamman a Chana, inda a can ne fara bulla.

Zuwa yanzu kasashe 44 ne suka bada labarin kamuwa da cutar, inda bayan Chana, a kasashen Turai ta fi muni a Italy. A yankin Asia kuma, Iran ce ta fi muni, inda har Mataimakin Ministan Lafiya da Mataimakiyar Shugaban Kasa suka kamu.

“Ganin yadda aka fara samun rahoton bullar Coronavirus a Lagos, to bari na bai wa gwamnatin Muhammadu Buhari shawara ta kishin kasa.

“Idan mu na son yin galaba a kan Coronavirus, to tilas sai mun tashi tsaye mun yi irin yadda gwamnati ta yi cikin 2014.

“Domin a lokacin an samu kyakkyawan hadin kai tsakanin gwamnatin tarayya da Jihohin Lagos da Rivera. Dalili kenan Najeriya ta zama a Afrika ita ce kasa ta farko wadda ta fara kakkabe cutar Ebola.

“Ina bada kwakkwarar shawarar cewa a dukufa aiki kawai, kasa a tsaya ana nune-nunen wanda ke da laifin shigo da matsalar. Idan ma wani za a nuna, to a nuna mana hanya mafita kawai. Ba wait a tsaya ana zargin wani ko wasu ba.

” Baya bayan nan mun rufe kan iyakoki domin veto tattalin arziki. To yanzu kuma ya kamata a gaggauta hana sauka filayen jiragen saman Najeriya daga kowace kasa, kuma a hana jirage tashi daga Najeriya. Tattalin arziki ba mai dorewa ba ne a lokacin da al’ummar kasa ke mutuwa.” Inji Atiku.

Cikin wannan sanarwa da ya fitar, ya ce ya zama tilas a gaggauta saka na’urorin binciken tantance mai dauke da cutar a filayen jiragen saman kasar nan.

A karshe ya ce kada hankulan ‘yan Najeriya ko na gwamnati ya tashi, idan dai aka sa kwazo da himma, kamar yadda gwamnatin baya ta yi wa cutar Ebola rubdugu, to babu shakka a wannan karon ma zaxa dakile Coronavirus cikin gaggawa.

Share.

game da Author