#CORONAVIRUS: Masana kimiyya sun fantsama kirkirar Maganin cutar

0

Hukumar Kula da Lafiya da ke karkashin Majalisar Dinkin Duniya, ta bada sanarwar cewa masana daban-daban na duniya, sun fantsama kirkiro sinadaran magance cutar Conronavirus.

WHO ta ce har ma wasu masu aikin kirkirar magungunan sun kai ga matakan yin gwaje-gwajen gane tabbaci da kuma ingancin kwayoyin maganin.

Da ya ke har yau babu takamaimen maganin cutar, ya zuwa Asabar ta yadu a kasashe har 49, kuma sama da mutum 2,000 ne cutar ta kashe daga Disamba zuwa karshen watan Maris.

Kasashen Denmark, Estonia, Lithuania, Netherlands da Najeriya duk sun bayyana an kamu da cutar daga kasar Italy a cikin kasashen su.

Ita ma Iran kamar yadda jami’in WHO mai suna Ghebreyesus ya bayyana, mutum 92 daga cikin daruruwan da suka kamu, duk daga waje aka shigar musu da ita.

Tun bayan bullar cutar ce Hukumar Lafiya ta Majalisar Dunkin Duniya (WHO) ta hada kai da Chana, su na hakilon nazarin ainihin yadda cutar ke shiga dan Adam, daga inda can ne asalin ta da kuma irin yadda ta ke mamayewar jiki da kuma irin illar da take yi.

Tun bayan barkewar cutar ne WHO ke ta kokarin wayar da kan kasashen da ta bulla da inda ba ta bulla ba, wajen sanar da su hanyoyin bi domin kauce wa wannan cuta da ta zama ruwan-dare cikin watanni uku.

WHO ta ce ta na wannan kokarin ne kafin jiran magungunan da masana suka dukufa binciken samarwa da kirkirowa.

Shaci-fadin da ake yi game da cutar #coronavirus

1. Wai idan mutum ya kanga hannu a na’ura mai busar da laima bayan wanke hannu, za a yi maganin cutar.

2. Wai hasken fitila mai hasken ‘ultraviolet’ na kashe cutar Coronavirus.

3. Wai idan aka watsa ruwan barasa ko sinadarin ‘chlorine’ za su yi maganin cutar Coronavirus.

4. Wai duk wanda ya bude wani dauri ko kunshin kaya daga Chana, zai kamu.

Ba gaskiya ba ne. Cutar Coronavirus ba ta dadewa jikin wani abu har ta day dogon lokaci. Sai fa jikin mutum.

6. Wai za a iya kamuwa da cutar daga jikin karnuka ko maguna.

WHO ta ce wannan ma karya ce.

7. Wai maganin cutar limoniya na magance Coronavirus.

8. Wai sai masu shekaru da yawa ta ke Kanawa.

Wannan ba gaskiya ba ne, ta na kama kowa, yaro da babba.

8. Wai kwayoyin maganin kashe cututtuka na kashe Coronavirus.

Ba gaskiya ba ne. Kwatoyin ‘antibiotics’ ba su kashe cutar Coronavirus.

9. Idan ta kama mutum ana shan maganin a warke.

To har yanzu dai babu takamaimen maganin ta. Amma akwai wadanda aka kula da su a asibitoci, suka warke, kuma aka sallame su.

Share.

game da Author