CORONAVIRUS: Kasar Saudiyya ta dakatar da bada Bizan shiga Kasar

0

Ma’aikatar Harkokin Kasashen Wajen Saudi Arabiya ta dakatar da bayar da Bizan shiga kasar ko don aikin Hajji, Umrah ko yawan shakatawa a dalilin barkewar cutar CoronaVirus da yake neman karade duniya.

Kasar Saudiyya ta ce ta dakatar da haka ne saboda ganin yadda a yanzu haka ma wasu kasashen dake makwabtaka da ita cutar ta fada musu.

Akalla akwai wadanda ke fama da cutar a kasashen Iran, Kuwait and Bahrain sannan kuma an tabbatar da akwai akalla mutane 240 da suka kamu da cutar a yankin gabas ta tsakiya.

Sannan kuma mahukuntar kasar sun dakatar da baiwa masu son zuwa aikin Umrah daga kasashen da cutar ta fada musu da kuma wasu kasashen da ake rade-radin cutar ya kai ga su.

Kasar Saudiyya dai ta dauki wannan matakai ne domin kare mutanen kasar ta da baki da ke kasar kamuwa da cutar CoronaVirus. Sannan kuma akwai hadarin gaske idan aka ce za a bar muatane su shigo kasar ba tare da an yi la’akari da hadarin dake ciki ba musamman a lokacin aikin hajji da bubban mutane ke dafifi a kasar domin aikin bauta.

Dukada cewa ana samun raguwar cutar a Kasar Chana inda nan ne ta fara bullowa, CoronaVirus na ci gaba da yaduwa a wasu sassan nahiyoyin duniya, da ya hada da yankin Gabas Ta Tsakiya.

Kasar Iran ita ce ke kan gaba da yawan wadanda suka kamu bayan Chana. Akalla mutane 22 sun rigamu gidan gaskiya sannan wasu 14i sun kamu da cutar ciki har da ministan Lafiyar kasar.

A kasar Iraq kuma, an samu wasu mutane da suka kamu da cutar, sai dai gwamnatin kasar ta dangantashi da matafiya dake barkowa daga kasar Iran suna shigo musu.

Gwamnatin Kasar ta bada umarnin a rufe manyan makarantun kasar na kwanaki 10 domin a gano bakin zaren don kada ya mamaye ko-ina.

Share.

game da Author