CORONAVIRUS: Kamfanin kera wayar IPhone ta dakatar da aiyukkanta a kasar Chana

0

A dalilin cigaba da yaduwar cutar Coronavirus a kasar Chana, kamfanin kera wayan sallula IPhone ta dakatar da aiyukkanta a kasar Chana.

Kamfanin ta sanar da haka ne a wata takarda da ta raba wa manema labarai a kasar ranar Litini.

Kamfanin ta bayyana cewa ta yanke haka ne ganin yadda yaduwar cutar Coronavirus ta kawo cikas wa kasuwar wayan Salula a duniya.

Ta ce ci gaba da aiki a cikin wannan yanayi da kasar ke ciki zai kawo wa kamfanin dimbin hasara.

“ Aiyukkan kasuwanci ya tsaya domin mutane na tsoron fita waje saboda kada su kamu da cutar. Haka ya kawo koma bayan tattalin arziki a kasar matuka.

“Dama mun yi hasashen cewa daga watan Janairu zuwa Maris kamfanin za ta yi cinikin akalla dala miliyan 67 amma a dalilin wanna cuta, hakan ba zai yiwu ba. Komai ya tsaya cak.

Kamfanin ta kuma ce za ta kara yawan tallafi na gudunmawa ga gwamnatin Chana domin kawo karshen wannan ibtila’i da ya fado mata.

Yaduwar CoronaVirus

Har yanzu dai cutar tana ci gaba da yaduwa a ciki da wajen kasar Chana.

A rahoton da take badawa game da cutar a kullum kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta bayyana cewa tsakanin ranar Lahadi da Litini mutane 1,772 ne suka rasu a dalilin cutar a kasar Chana.

Kungiyar ta kuma ce a cikin awowi 24 wasu mutane 2,051 sun kamu da cutar a kasar.

Sakamakon binciken da kungiyar ta gudanar ya nuna cewa kashi 94 bisa 100 na mutane na kamuwa da wannan cuta ne daga Lardin Hubei dake Wuhan.

Cutar ta yadu zuwa kasashe 25 inda har ya yi ajalin mutane uku.

Kwayoyin cutar Corona Virus na daga cikin kwayoyin cutar dake sa a kamu da mura wanda idan yayi tsanani akan yi fama da matsalar cutar dake hana numfashi yadda ya kamata da ake kira (Middle East Respiratory Syndrome (MERS-CoV), da kuma cutar tsanannin mura da kan toshe makogoro.

Akan kama cutar ne a dalilin cudanya da dabbobi domin sune ke dauke da ita. Sakamakon bincike da aka yi game da cutar ya nuna cewa akan kamu da cutar ne ta hanyar yin muamula da dabbobi na gida da na daji.

Alamun kamuwa da cutar sun hada da matsala a kafofin wucewar iska a makogoro wato numfashi, yawan zazzabi, tsananin tari, da ciwo a makogoro.

Haka kuma idan abin yayi tsanani, ya kan kai ga shakar iska ma ya gagara, sannan a samu matsalar sanyin hakarkari wato ‘Nimoniya’, kuma idan har ya yi tsanani matuka kodar mutum kan daina aiki kwata-kwata.

Share.

game da Author