CORONAVIRUS: Dan Najeriya mai buga kwallo a Juventus ya kamu

0

An samu dan Najeriya na farko ya kamu da cutar Coronavirus a kasar Italy. Paul Akpan Udoh ya na wasa ne a kungiyar kwallon kafa ta su Cristiano Ronaldo, Juventus, Amma a yanzu an bada shi aro (lamuni) ne ga kungiyar Pontedera.

Ranar Alhamis aka yi masa gwaji, aka tabbatar da ita. Sannan aka gaggauta killace shi, don kada wasu su kamu.

Idan ba a manta, Baturen da aka samu da cutar Coronavirus shi ma daga kasar Italy ya shigo Lagos, Najeriya, a ranar Talata.

Udoh ya yi wasa a karamin kulob din Juventus, bayan ya bar Reggiana cikin 2011. Daga nan kuma ya yi wasa a Lanciana, ya koma Pontedera, ya bugs kwallo a Farriana, Fano da Viareggio, kafin komawa Piarese cikin 2019.

Amma dai har yanzu a matsayin dan wasan Juventus ya ke, wanda ta bada aro ga wasu kananan kulob daban-daban na kasar Italy.

Akalla mutum sama da 400 aka bada rahoton sun kamu da Coronavirus a Italy. Kuma ita ce kasar Turai kakaf, wadda cutar ta fi yi wa mamayar ba-zata.

Zuwa yanzu dai kasashe kamar su Iran, Iraq da Japan sun rufe makarantu da wata daya. Najeriya ma wani dan kasar Italy dinne ya tsallako da ita kasar.

Shima yana can an killace shi a wani wuri.

Share.

game da Author