Shugaban Hukumar EFCC, Ibarahim Magu, ya bayyana cewa cin hanci da rashawa ne suka haddasa barkewar cutar ‘Corornavirus’ a duniya.
Magu ya yi wannan ikirarin ne a gaban Shugaba Muhammadu Buhari, a lokacin da ya ke jawabi wurin bukin yaye Kwararrun Jami’an EFCC su 281, da suka yi horon Kwas na Insifeto Masu Bincike a NDA, Kaduna.
“Cin hanci da rashawa sun fi kowace irin cuta yi wa mutum illa da lahani a duniya.
“Mai Girma Shugaban Kasa, ni dai na yi imani cewa hatta cutar ‘coronavirus’ da ta addabi China da dasuran wasu kasashe a yanzu, to cin hanci dac rashawa ne suka haddasa ta.
“Yaki da cin hanci da rashawa tamkar jihadi ne akan wasu shaidanun mutane, saboda rashawa bala’i ce wadda ke neman gamawa da mu.
“Akwai jidali sosai a yakin da cin hanci da rashawa, amma duk da haka mu na samun nasara da yin galaba sosai wajen dakile ta da murkushe masu yin wannan aika-aika.” Inji Magu.
Sai dai kuma Magu har ya gama jawabin sa, sai kawo misali ko hujja ko guda daya da ya bayyana wa dimbin jama’ar da ke wurin hujjar cewa cin hanci da rashawa din ne suka haddasa cutar coronavirus ba.
PREMIUM TIMES ta bada labari a baya bayan nan cewa cutar coronavirus, wadda ta fara bulla a birnin Wuhan da ke Gundumar Hubei na China, ta kashe mutane sama da 1,773 a China da sauran kasashen duniya sama da 30.
Ko cikin makonni biyu da suka gabata, sai da Hukumar Kula da Lafiya ta duniya, WHO ta kaddamar da kokon barar kafa gidauniyar neman tallafin kudi dala milyan 675, domin a gaggauta tarbar cutar da wuri, kada a bari ta kai ga shiga kasashen da ba su da kwakkwaran tsarin kula da lafiya a duniya.
Hamshakin attajiri Bill Gates dai tuni ya bayar da gudummawar dala milyan 100, ta hannun Gidauniyar sa ta Bill and Melinda Gates.
Discussion about this post