Cikin barkwanci, Shehu Sani ya yi wa Soyinka lakani da “Shugaban masu aikata laifi”

0

Sanata Shehu Sani ya yi wa Wole Soyinka lakani da “Shugaban Masu aikata laifi a Najeriya”.

cikin barkwanci tsohon sanatan ya fadi haka ne a cikin kotu a lokacin da su kayi gangami domin raka Sowore kotu a ci gaba da shari’ar sa da ake yi a Abuja.

Shi da kansa ya saka bidiyon a shafinsa na Tiwita, inda a bidiyon dukkan su suka kwashe da dariya bayan ya fadi haka.

Kotun ta cika ta batse da jigajigan masu rajin kare hakkin dan Adam da suka hada da tsohon shugaban kare hakkin dan Adam Chidi Odinkalu da sauransu.

Wole Soyinka ya raka Sowore kotun domin sautraren yadda za ta kaya.

Sai dai kuma kuton bata dade a zaman ta ba domin masu daukaka kara basu halarci zaman kotun ba.

A dalilin haka kotu ta ce umarci ministan Shari’a, Abubakar Malami da ya biya Sowore naira 200,000 saboda bata wa Sowore lokaci da suka yi sannan basu halarci zaman kotun ba.

Share.

game da Author