Da sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin Kai
Dukkan kyakkyawan yabo da godiya su tabbata ga Allah. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad (SAW), da Iyalan sa da Sahabban sa baki daya.
Ya ku al’ummah, Abu Bakrata (RA) ya hakaito cewa wani mutum ya tambayi Manzon Allah (SAW) yace, “ya Manzon Allah (SAW), a cikin mutane baki daya wane mutum ne yafi daraja da falala?” Sai Manzon Allah (SAW) yace: “Wanda yafi daraja da falala shine, wanda yayi tsawon rai kuma ya kyautata ayukkan sa.” Sai wannan mutum ya sake tambayar Annabi (SAW) cewa, “to kuma wane mutum ne mafi zama mutumin banza a cikin mutane?” Sai Annabi (SAW) yace, “shine wanda yayi tsawon rai, kuma ayukkan sa suka munana.” [Tirmidhi ne ya ruwaito shi]
Sannan Abdullahi Ibn Busr ya hakaito cewa, wani balaraben kauye ya tambayi Manzon Allah (SAW) cewa, “ya Manzon Allah (SAW), wadanne mutane ne suka fi matsayi, da daukaka, da daraja da falala?” Sai Manzon Allah (SAW) yace, “wanda yayi tsawon rai kuma yayi aiki mai kyau.” [Tirmidhi ne ya ruwaito shi]
‘Yan uwa na masu girma, wadannan Hadisai suna karantar da mu ne fa’idah tare da muhimmancin Allah Subhanahu wa Ta’ala ya albarkaci bawan sa da yawan shekaru da tsawon rai mai albarka. Ashe kenan, a Musulunci, mutumin da yayi tsawon kwanaki, kuma ya tafiyar da su akan tafarkin da Allah yake so, tafarkin addini da taimakon bayin Allah, irin wadannan mutane su ake nema, kuma sune abun alfahari, kuma su ake bukata a cikin rayuwa.
Mutumin kuwa da yayi tsawon rai mara amfani, yayi shekarun banza, irin wannan mutum sam al’ummah ba ta bukatar sa! Domin rayuwar sa ba ta zama mai amfani ga kowa ba!!
Ya ku ‘yan uwa, Mai Martaba Sarkin Zazzau, Alhaji (Dr.) Shehu Idris, yana daga cikin mutanen da Allah Subhanahu wa Ta’ala ya albarkace su da tsawon rai mai albarka, rayuwar da ta zama mai albarka kuma mai amfani ga al’ummah.
Ranar Asabar da ta gabata ne aka yi bikin cikar Mai Martaba Sarkin Zazzau, Alhaji (Dr.) Shehu Idris, shekara arba’in da biyar (45) a kan gadon sarauta.
Alhaji Shehu Idris shine Sarki na 18 da ya dare kan mulkin Zazzau tun bayan jihadin Shehu Usman Danfodio.
An nada shi a kan mulki ne a shekarar 1975 bayan rasuwar Sarkin Zazzau, Alhaji Muhammadu Aminu.
Tun ranar Juma’ah 7 ga wata ne aka soma shagulgula, a inda aka gabatar da addu’o’i a Masallatan kasar Zazzau da jihar Kaduna baki daya.
Kuma an gudanar da kasaitaccen bikin hawan dawaki, wato durbar.
Masarautar Zazzau dai na cikin manyan masarautun Najeriya kuma tana cikin abin da masana suka kira Hausa Bakwai.
Mai Martaba Sarkin Zazzau, Alhaji (Dr.) Shehu Idris yana daya daga cikin manyan Sarakunan Arewancin Najeriya. Kuma shi mutum ne masani, sannan kuma abin girmamawa a duk fadin arewa da Najeriya da ma duniya baki daya. Sannan Mai Martaba mutum ne mai hakuri, mai karimci. Daya daga cikin dimbin hikimomi da Allah ya yiwa Mai Martaba Sarkin Zazzau, Alhaji (Dr.) Shehu Idris ita ce iya tafiya da mutane cikin ruwan sanyi a cikin mulkinsa, domin yakan tuntubi jama’ah a kan abubuwan da ka-je-su-komo.
An haifi Mai Martaba Sarkin Zazzau, Alhaji (Dr.) Shehu Idris a shekarar 1937. Shi da ne ga Malam Idris Autan Sambo, shi kuma dan Sarkin Zazzau na goma, Malam Muhammadu Sambo, shi kuma dan Sarkin Zazzau na uku Malam Abdulkarimu Bakatsine.
Mai Martaba Sarkin Zazzau, Alhaji (Dr.) Shehu Idris, ya fara karatunsa na addini tun yana dan shekara biyar a hannun Malam Bawa da kuma Malam Abubakar da ke Unguwar Iya a garin Zariya. A shekarar 1947, lokacin yana da shekaru goma sha daya, Mai Martaba Sarki ya fara karatun zamani a makarantar elimantare ta Zariya (wato Zaria Elementary School), daga nan kuma sai makarantar midil ta Zariya (wato Zaria Middle School) daga shekarar 1950 zuwa 1955. Bayan kammala wannan karatu nasa sai kuma ya wuce zuwa makarantar horas da Malamai ta Katsina (wato Katsina Training College) inda ya gama a shekarar 1958.
Mai Martaba Sarkin Zazzau, Alhaji (Dr.) Shehu Idris, ya fara aikin karantarwa bayan kammala karatunsa na Katsina. Ya fara da koyarwa a makarantar firamare ta garin Hunkuyi a shekarar 1958, daga nan kuma sai aka mayar da shi garin Zangon Aya, sannan sai Paki duk a matsayin shugaban makaranta (wato Head Master). Sannan kuma aka dawo da shi Zariya a matsayin shugaban makarantar firamare ta Ƙaura.
A shekarar 1960 ya zama magatakardar Sarkin Zazzau Marigayi Alhaji Muhammadu Aminu (wato Personal Secretary to the Emir of Zazzau). Daga baya kuma ya zama magatakardar Hukumar gargajiya (wato Secretary to the Zaria Native Authority council) a shekarar 1963. Sannan kuma an yi masa nadin Dan madamin Zazzau, Hakimin Birni da Kewaye a shekarar 1963, mukamin da ya rike har zuwa zamowarsa Sarkin Zazzau.
A shekarar 1975, bayan rasuwar Mai Martaba Sarkin Zazzau Alhaji Muhammadu Aminu, sai masu zaben Sarkin Zazzau (wato King Makers), suka zabi Mai Martaba Sarki Alhaji (Dr.) Shehu Idris a matsayin sabon Sarkin Zazzau, zaben da ya samu amincewa daga gwamnatin Jihar Tsakiyar Arewa wadda ke da helikwata a Kaduna, a zamanin mulkin Gwamna Manjo Abba Kyari. Wannan nadi nasa shi ya mai da shi Sarkin Zazzau na 18 a jerin Sarakunan Fulani, sannan kuma Sarki na uku a zuriyar Katsinawa.
Saboda gudunmawa da ya dade yana bayarwa, musamman ta fuskar kira game da zaman lafiya, ilimi da hadin kai, Mai Martaba Sarkin Zazzau Alhaji (Dr.) Shehu Idris ya karbi lambobin yabo da girmamawa da dama daga ciki da wajen Najeriya. Daga cikin irin wadannan lambobi akwai digirin girmamawa na digirin-digirgir (wato Dr.) da ya karba daga jami’o’in Minna (wato Federal University of Technology, Minna), jami’ar Najeriya ta Insuka (wato University of Nigeria, Nsuka), Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya (wato Ahmadu Bello University, Zaria), da kuma jami’ar Abuja (wato University of Abuja).
Sannan a shekarar 2006, Ƙungiyar dalibai ta Jami’ar Ahmadu Bello (wato ABU Alumni Association Award) ta bashi lambar yabo ta ‘Distinguished Service Award.’
Shekara arba’in da biyar (45) na Mai Martaba Sarkin Zazzau Alhaji (Dr.) Shehu Idris a kan gadon mulki Allah ne ya azurta al’ummar Masarautar Zazzau da wannan bawa nasa. Tun lokacin da Allah ya dora shi a karagar mulkin Zazzau, babban abin da yasa a gaba shine, ganin al’ummar sa ta ci gaba, tare da kokarin samar da zaman lafiya. Domin yayi amanna cewa, babu wani arziki da zai samu ga al’ummah, face sai da zaman lafiya. Sauran abubuwan da Mai Martaba yasa a gaban sa dare da rana a cikin shekara 45 din nan, shine, kokarin ganin cewa al’ummar sa sun tashi tsaye wurin neman ilimin addini da ilimin zamani da kuma samun sana’ar dogaro da kai, kuma duk yana yin haka ne domin al’ummah ta ci gaba, kuma ni ina da tabbacin cewa lallai burin sa ya cika, tun da an sami zaman lafiya, musamman a Masarautar Zazzau, da kuma jihar Kaduna, da ma Nijeriya baki daya, ba kamar can da ba. Kuma duk wanda yazo birnin Zariya, ya san an sami ci gaba ta fuskar samar da makarantu daban-daban, kuma tun kafin zuwan turawa, Masarautar Zazzau ta sami bunkasa a fagen ilimin addini, da kuma sana’o’in dogaro da kai. Don haka, babu abin da Zage-zagi za su ce da Mai Martaba Sarki, sai addu’ar Allah ya kara masa lafiya. Sannan kuma ina rokon Allah ya kara masa masu ba shi dukkan shawarwarin da suka dace, domin ci gaban Masarautar Zazzau da jihar Kaduna da ma Najeriya baki daya, amin.
Kuma mu sani cewa, har kullun, Mai Martaba Sarkin Zazzau, yana umurtar al’ummar sa da su zama masu tattalin zaman lafiya, tare da kuma bada gudummawa, na ganin cewa an tallafa wa al’ummah a ko wane mataki na rayuwa. Mai Martaba Sarki, a kowane lokaci yana umurtar ‘ya ‘yan sa da jama’ar kasar Zazzau baki daya, da su zamo masu son mutane a duk inda suka samu kan su, tare da zama masu saukin kai ga duk wanda ya je gare su, a matsayin su na ‘ya’yan sa, jama’ar sa, da kuma hakiman sa. Saboda haka ne ma yasa mutanen kasar Zazzau suka fi kowa murna, ganin yadda kowa ke murna da jin dadi, na irin yadda Mai Martaba Sarki yake jan karagar mulkin kasar Zazzau. Kuma suna ta nuna godiya ga al’ummar Masarautar Zazzau na yadda ake ba wa Mai Martaba goyon baya tare da addu’o’i da ake yi masa ako wane lokaci, kasancewar sa Sarki mai adalci.
Wannan yasa ya zama wajibi ga dukkanin al’ummar Masarautar Zazzau, su ci gaba da godiya ga Allah, da ya basu wannan Sarki da babu abin da ke cikin zuciyar sa sai adalci da hangen-nesa ga duk wasu al’amurra da suka taso a Masarautar Zazzau da kuma Najeriya baki daya.
Duk lokacin da Mai Martaba Sarki zai yi jawabi, furucin sa na farko shine, ayi tattalin zaman lafiya, wannan batun da yake yawan furtawa, kowa yasan yana yin tasiri wurin ci gaban zaman lafiya da ake samu a Masarautar Zazzau da kuma kasa baki daya. Kuma yana yawan cewa, Zazzagawa ku zama tsintsiya madaurinki daya a duk inda aka tsinci kai. Wannan kira yasa Mai Martaba Sarkin Zazzau ya zama madubi ga duk wani batu da ya shafi zaman lafiya a Najeriya, ba Masarautar Zazzau kawai ba.
Yadda ake samun wasu matsaloli na rashin tsaro a wasu sassan jihar Kaduna, Allah ya kare Masarautar Zazzau a shekaru da dama, inda aka sami dauwamammen zaman lafiya a tsakanin al’ummar lardin Zazzau. Kuma duk fadin jihar Kaduna, Masarautar Zazzau na da manyan makarantun fannoni da dama, wannan duk yana nuna muna cewa, ayukkan kishi ne da irin jajircewa da Mai Martaba Sarkin Zazzau ya nuna, shi yasa aka sami wadannan cibiyoyin ilimi a yankin Masarautar Zazzau. Don haka har kullun, ina addu’ar Allah ya kara wa Sarki lafiya, da kuma jinkiri mai amfani ga dukkan al’ummar Najeriya baki daya, ba Masarautar Zazzau kawai ba, domin mu ci gaba da amfana da irin salon mulkin adalci da yake yiwa al’ummar Masarautar Zazzau.
Kai hatta ma ‘yan kasuwar kasar Zazzau, babu abin da za su yiwa Mai Martaba Sarki, illa addu’o’in karin lafiya da kuma fikirar ci gaba da jagoranci nagari, domin kuma yaci gaba da zama abin koyi ga sauran Sarakuna da suke sassan Najeriya. Sannan kowa ya shaida cewa, kirarin da ake yiwa Sarki na balaraben Sarki, abu ne da yayi dai-dai da rayuwarsa kafatan.
Don haka cikar Mai Martaba Sarkin Zazzau shekara 45 bisa gadon mulki muhimmin abu ne da ko wane Ba-Zazzagi da duk ‘yan Najeriya ya kamata suyi addu’a akai, da kuma fatan Allah ya karawa Sarki lafiya, domin ya sami iko da damar aiwatar da jagoranci nagari da yake yi a shekara 45 da suka gabata.
Lallai ni a iya sani na, bayan Sarkin Zazzau Malam Ja’afaru Dan Isiyaku, tun da ake Sarakuna a Masarautar Zazzau, ba’a taba samun Sarki mai ilimi, mai hakuri da hangen nesa da kuma kau da kai ga duk wasu abubuwan da kana ganin zasu bata masa rai, amma ba zaka gani ko kaji wasu batutuwa sun fito daga bakin sa ba da suka shafi bacin rai, ko kuma wasu kalmomi da za su raba kan al’ummah ba. Ga kuma kau da kai daga dubon duk wani ko kuma wasu abubuwa da za su sa al’ummah su fahimci zuciyar sa ta baci.
Mai Martaba Sarkin Zazzau uba ne ga kowa da kowa, kuma shi mai bayar da muhimmanci ne ga duk wani batu da ya shafi ilimi da ci gaba, ba a Masarautar Zazzau kawai ba, a’a, duk fadin Najeriya baki daya, musamman irin lura da yadda a tsawon mulkin sa aka sami ci gaba a makarantu na fannoni da dama, wanda daliban da suke karatu a wadannan makarantu, ba ‘yan asalin zazzau ne kawai ba.
A duk lokacin da Mai Martaba Sarki ya bude baki yake jawabi, batutuwan da yake fadi basu wuce maganar tattalin zaman lafiya ba, sai kuma batun cewa a tashi tsaye a nemi ilimi a sauran fannonin ilimi da za su sa a daina yiwa ‘yan arewa kallon hadarin kaji. Kuma mutum zai kara fahimtar Mai Martaba Sarkin Zazzau a matsayin shugaba nagari abin koyi ta ko wane bangare na shugabanci. A matsayin sa na tsohon Malamin makaranta kuma masanin mulkin al’ummah, wanda wadannan abubuwa biyu sune suka sa Mai Martaba Sarki ke jan silin mulkin sa da kowa yake na’am da shi.
Cikar Mai Martaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris shekara 45 a matsayin Sarkin Zazzau, kai da baki dayan rayuwar sa, wallahi karatu ne mai zaman kansa, musamman, a bangarorin hakurin sa da hangen nesan sa da kuma yin jawabin da ke kwantar da kowace irin matsala in ta taso, kuma ko da ba a Masarautar Zazzau ba ne.
Kamar dai yadda bayani ya gabata, a ranar takwas ga watan Fabrairun shekarar 1975 ne mai girma Hakimin Birni da Kewaye a wancan lokaci, wato shi Alhaji (Dr.) Shehu Idris, Allah ya tabbatar masa da sarautar Masarautar Zazzau baki daya, wanda kenan a ranar Asabar da ta gabata ne, wato takwas ga watan Fabrairu na wannan shekara ta 2020, Mai Martaba Sarki ya cika shekara arba’in da biyar (45) da hawa karagar mulkin Masarautar Zazzau. A kan haka ne naga dacewar in kasance cikin masu yin addu’o’i tare da fatan alkhairi ga mai martaba Sarki, tare da masarauta da al’ummar kasar Zazzau baki daya, akan Allah ya taimaki Sarki, ya kara masa lafiya da nisan kwana, tare da shekaru masu albarka. Kuma ina rokon Allah ya taimaki dukkanin ‘yan majalisar Sarki, ya kara masu lafiya da karfin imani, musamman baban mu, Mai girma Yariman Zazzau, Alhaji Munir Ja’afaru, saboda irin gudummawa da yake bai wa addinin Musulunci da Musulmi baki daya, a duk tsawon rayuwar sa mai albarka. Allah ya ja zamanin sa, ya kara masa lafiya da nisan kwana, amin. Haka ma ina rokon Allah Subhanahu wa Ta’ala da yaci gaba da kare Masarautar Zazzau, tare da dukkanin Masarautun mu, daga dukkanin sharri da fitina, na fili da na boye, wadanda muka sani da wadanda ba mu sani ba, amin.
Muhimman Takaitattun Abubuwan Da Ya Kamata Mu Sani Game Da Rayuwar Mai Martaba Sarkin Zazzau, Alhaji (Dr.) Shehu Idris:
1. A ranar 20 ga watan Feburairu 1937 aka haifi Sarki Shehu Idris.
2. Shekarun Sarkin Zazzau Shehu Idris 83.
3. Sunan mahaifin Sarki Malam Idris Autan Sambo.
4. Sunan mahaifiyar Sarki Hajiya Aminatu.
5. A ranar 8 ga watan Feburairu 1975 aka nada shi Sarkin Zazzau.
6. Sarki Shehu Idris shine ya gaji Sarkin Zazzau Muhammadu Aminu.
7. Sarki Shehu Idris shine Sarki na 18 a Masarautar Zazzau.
8. Mahaifin Sarki Shehu Idris ya rasu yana dan shekara 12.
9. Kakansa da Kakan babansa dukkaninsu sun yi sarautar Zazzau.
10. Kakansa, Sarki Muhammadu Sambo ya mulki Zazzau daga 1879 zuwa 1888.
11. Kakan babansa, Sarki Abdulkarimi ya mulki Zazzau daga 1834 zuwa 1846.
12. Sarki Shehu Idris yayi karatun ilimentari daga 1947 zuwa 1950.
13. Sarki Shehu Idris yayi makarantar Zariya Midil daga 1950 zuwa 1955.
14. Sarki Shehu Idris yayi karatu a makarantar horas da malamai ta Katsina.
15. Sarki Shehu Idris ya koyar a Hunkuyi a shekarar 1958.
16. Sarki Shehu Idris ya zama sakataren Sarki Aminu a shekarar 1960.
17. Sarki Shehu Idris ya zama sakataren hukumar mulki ta Zariya a 1965.
18. Sarki Shehu Idris ya zama Dan Madamin Zazzau a shekarar 1973.
Littafai da rubuce-rubucen da na dogara da su domin wannan rubutu sun hada da:
1. Malam Ja’afaru Dan Isyaku, The Great Emir of Zazzau. Woodpecker Communication Limited. Zaria-Nigeria, by Dalhatu U. (2002).
2. Categories of ABU Alumni Association Award, by Jika A. (2016).
3. As Emir of Zazzau Bags Another Doctorate Degree, by Suleiman A. (2016).
4. Shehu Idris: 41 Years of Purposeful Rulership, by Suleiman A. (2016).
5. Wikipedia (2016). Under the name Shehu Idris.
6. Kafafen sadarwar zamani na Intanet, mujallu da jaridu.
Ina rokon Allah ya kyauta, ya taimake mu, yayi muna jagora, ya kawo muna mafita ta alkhairi, amin.
Dan uwan ku, Imam Murtadha Muhammad Gusau, ya rubuto daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za’a iya samun sa a lambar waya kamar haka: 08038289761.