Buhari ya yi Allah-wadai da kasashen da ke ruruta rikicin Libya

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi Allah-wadai da irin yadda ake samun masu ruruta wutar rikicin Libya, wanda a kullum sai kara muni ya ke yi.

Ya nuna damuwa ganin yadda rikicin ya ki ci ya kuma ya ki cinyewa, sannan kuma kai tsaye ya na shafar kasashen yankin Sahel, wadanda Najeriya na cikin su.

Buhari ya yi wannan jawabi a taron Majalisar Tsaro ta Kungiyar Kasashen Afrika a kan matsalar Libya da Sahel, wanda ke gudana a Addis Ababa, babban birnin Ethiopia.

Buhari ya na wurin taron tun a ranar Juma’a, inda ya tashi daga Abuja tare da ayarin ‘yan rakiya, da suka hada da gwamnoni da ministoci.

Ministan Harkokin Kasashen Waje na Najeriya, Geoffrey Onyeama ne ya wakilci Buhari, kuma ya karanta bayanin sa a wurin taron.

“Duk da irin kokarin da daukacin kasashen da ke cikin Kungiyar Hadin Kan Afrika ke yi wajen shawo kan rikice-rikicen Libya da na yankin Sahel, wasu masu bakar aniya daga waje na yin katsalandan a rikicin Libya, ta yadda al’amarin ke ta kara tabarbarewa.

Daga nan ya yi kira da a samar da sabon tsarin da zai taimaka wajen ganin an shawo kan rikicin, maimakon ya rika kara tabarbarewa.

“Mu na yin Allah-wadai da yadda ake samun katsalandan daga waje, domin shaidar cewa akwai sojojin haya daga wata kasa a Libya, ya tabbatar da haka.

“Kasa dakile rikicin Libya kai tsaye ya haifar da matsaloli sosai. Musamman yadda ake amfani da sojojin haya da kuma rabuwar kawunan manyan hukumomi da cibiyon duniya.

Buhari ya nuna rashin jin dadin yadda Majalisar Dinkin Duniya ta ba amnce da tura jakadan hadin-guiwa tsakanin Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Kasashen Afrika zuwa Libya ba.

Share.

game da Author