Buhari ya roki masu wa’azi su maida hankali wajen nuna hada kan iyali da gina al’umma

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya roki masu wa’azi su maida hankali wajen wa’azantar da jama’a su fifita hadin kan iyali da kuma gina al’umma.

Ya ce masu wa’azi na musulunci da na kirista su tuna su ne bangon jingina kuma ginshikin gina al’umma tagari.

Da ya ke magana a wurin Taron Hadin Gwiwa na Majalisar Koli ta Musulunci (NSCIA) da kuma Kungiyar ‘Future Assured Initiative suka shirya, Buhari ya ce iyali su ne kashin bayan kowace al’umma, kuma ya ta cancanci ba ta kulawa sosai a duniya.

“A wannan yanayi, shugabannin addinan mu su ne ke kasancewa masu dora all’umma a kan turba, domin su ne rushin kowace al’umma. Sai ya ce lallai abin jin dadi da jinjina ne ganin yadda Majalisar Kolin Musulunci da ‘Future Assured’, ganin cea sun rungumi wannan kalubale.

“Ina kira ga sauran kungiyoyin addinin Musulunci da na Kirista su bi sawun da NSCIA da ‘Future Assured’ suka bi, ta hanyar sauya akalar tsarin wa’azantar da ake yi wa jama’a kan muhimmancin iyali.

“Mu na taka-tsantsan da yadda kuncin talauci ke biyiya da kuma yi wa iyali mummunar illa. Gwamnatin mu ta aiwatar, kuma ta bijiro ayyukan rage radadin talauci da dama.” Inji Buhari.

Ya kara da cewa wadannan ayyuka sun yi tasiri sosai wajen rage wa iyali matsalollin kunci da kuma kawo karshen fatara a cikin iyali da dama.

Ya ce gidaje da dama sun amfana da dimbi kudaden da gwamnati ta rika rabawa na tsarin tallafin iyali, ‘trader-moni’ da sauran tallafin rage zafi da kuncin talauci.

Ya kuma yi magana a kan irin tasirin da tsarin ciyar da ’yan makaranta ya samar da da mai ido sosai a kasar nan.

Ya kuma yi magana kan shirin kafa cibiyoyin sauraren korafe-korafen da suka jibinci sabani ko sa-in-sa tsakanin ma’aurata.

Share.

game da Author