Buhari ba zai sauka ba din – Inji Lai Mohammed

0

Ministan yada labarai Lai Mohammed ya gargadi shugabanin addinai da na siyasa da su iya wa bakunansu cewa kalaman da su ke yi za su iya tada zaune tsaye a kasar nan.

Lai ya bayyana cewa bayan haka kira da wasu ke yi na wai shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi murabus ko ya sauka daga kan gadon mulki, sun yi kadan domin ba zaman su yake yi ba, zaman duka ‘yan Najeriya ya ke yi da suka zabe shi, kuma yana na daram har har shekarar 2023.

” Sannan kuma maganan tsaro da ake ta cecekuce akai, gwamnati na kokarinta wajen ganin ta samar wa ‘yan kasa tsaro a ko-ina sannan kuma akwai tabbacin cewa ana samun nasara a harkar samar da tsaro a kasar nan.

” Tabbas za a kawo karshen matsalar tsaro a kasar nan kwata-kwata kuwa, sai ya zama tarihi a karkashin mulkin Buhari.

Baya ga haka yayi kira ga shugabannin addinai da ‘yan siyasa har ila yau da su rika furta kaman da zasu kawo hadin kai ne a kasar nan ba tashin hankali da ruruta rashin zaman lafiya da tsaro ba.

A karshe sai ya gwasale masu kira ga shugaba Buhari da yayi murabus a dalilin rashin tsaro da ya zame wa Najeriya Kashin kifi a wuya ya na mai cewa su yi karatun ta natsu su ma daina fadin haka domin Buhari na talakawa ne wadanda suka zabe shi. “Yana nan daram har zuwa 2023.”

Share.

game da Author