Boko Haram sun kashe malaman Boko 547 -Kungiyar Malamai

0

Kungiyar Malaman Makaranta ta Kasa (NUT), ta tabbatar da cewa Boko Haram ta kashe mambobin ta har 547.

Duk da dai NUT ba ta bayyana tun daga wane lokaci zuwa wane lokaci aka kashe mata wannan adadi mai yawa ba, ana ganin an yi wannan gagarimar asarar rayukan malaman tun daga farkon fara rigimar Boko Haram, sama da shekaru goma da suka gabata.

Kungiyar ta ce wannan adadi na malamai 547, an rasa su a jihohin Arewa maso Gabas kadai.

Kenan ba a lissafa har da na sauran jihohin Arewacin kasar nan ba kenan.

Sannan kuma NUT ba ta tantance yawan wadanda aka kashe a Barno, Yobe ko Adamawa ba.

Shugaban NUT Idris Nasir ne ya bayyana haka, a Abuja a ranar Talata, a Taron Majalisar Malaman Makarantu ta Kasa.

Daga nan Idris ya nuna takaicin yadda har yau gwamnati ba ta biya iyalan mamatan hakkokin su da ya kamata a biya ma’aikatan da suka mutu lokacin su na aiki ba.

“Karin abin haushi shi ne yawancin ‘ya’yan mamatan duk an koro su daga makaranta, saboda kasa biyan kudaden makaranta.

Ya yi roko ga Shugaba Muhammadu Buhari ya sa baki ga gwamnatin jihohin da malaman suka yi wa aiki a biya su hakkokin mamatan da gaggawa.

Daga ya sanar wa mahalarta taro cewa a ziyarar su ta baya da suka kai wa Buhari, ya amimce da kukan da suka yi masa cewa su ma a maida ritayar malaman makarantu zuwa shekara 65, kamar yadda aka maida na malaman jami’o’in kasar nan.

Share.

game da Author