Awowi kadan bayan ficewar shugaban Kasa Muhammadu Buhari daga garin Maiduguri Boko Haram sun afkawa wa mutanen unguwar Jaddiri inda suka yi ta barin harsashi suna cinna wa gidaje wuta.
Idan ba a manta ba ko da shugaba Buhari ya isa garin Maiduguri, mutane da dama sun fito gefen manyan titunan babban birnin suna yi masa ihun “Bamu su so, Bamu so.”
Wani shugaban ‘yan banga da ke aiki a wannan unguwa da Boko Haram suka kai farmaki dake kusa da titin Polo dab da baban Kotun Maiduguri ya bayyana cewa maharan sun far wa unguwan ba tare da sun tsagaita barin harsashi ba har suka fice.
Ba’Bulama Jiddari ya kara da cewa haka nan suma suka fito suka tunkari maharan tare da taimakon sojoji da suka zo daga baya har suka iya kora su suka fice daga garin.
Sai dai kuma ya ce har yanzu basu iya tantance yawan mutanen da aka rasa ba. ” Mun dai ga sun cinna wa wani gida wuta.”
Ita ko Rebbeca Musa, wadda mazauniyar wannan unguwa ce ta shaida mana cewa bata taba ganin fankon harsashi irin wanda ta gani ba.
” Wannan tashin hankali ya bani tsoro matuka domin ban taba ganin ana barin wuta irin haka ba. Duk ta inda ka duba harsashi zaka ci karo da wai kuma ace mintina kadan da ficewa shugaban kasa daga gari.
Wani dan banga ya yi korafin cewa sai da sojoji suka janye daga wannan yanki na jaddiri sannan Boko Haram suka far wa unguwar.
Discussion about this post