BOKO HARAM: Sakacin sojoji ne dalilin kisan matafiya 30 -Zulum

0

Gwamnan Barno Babagana Zulum ya dora laifin kisan mutane 30 da kona gidaje da motocin matafiya da Boko Haram suka yi a Auno, a kan abin da ya kira ma sakacin sojoji wajen kin maida hankali ga tsare Auno.

Zulum ya nuna bacin ran sa karara da fushi a safiyar Litinin, lokacin ya je garin Auno, ya gane wa idon sa irin mummunan kisan da Boko Haram suka yi wa matafiya a Lahadi da dare.

PREMIUM TIMES ta bayar da labarin yadda Boko Haram suka banka wa motocin matafiya wuta, suka arce da wasu matafiya, bayan sun kashe wasu da dama a Auno.

Mayafiyan sun yada Zango ne a Auno, kilomita 24 kusa da shingen tsaron sojoji kafin shiga Maiduguri.

Sojoji kan datse hanyar shiga Maiduguri tun 6 na yamma zuwa washegari, 6 na safe, babu shiga kuma ba fita.

“A gaskiya an tura ni har an kai ni bango. Tunda na kai makura, bari na fito na fadi gaskiya.” Inji Zulum.

“Daga ranar da aka rantsar da ni zuwa yau, Boko Haram sun kai hari a ganin Auno kamar sau shida kenan. Kuma dalili kawai shi ne saboda sun samu kofar kawo harin ne saboda sojoji sun janye daga Auno.

” Mun yi kira kuma mun sha yin roko ga sojoji su dawo da sansani, su kafa sansani a Auno. Amma ba su karbi roko ko shawarar mu ba har yau.”

Wani Kwamandan Bataliya da ke tare da Gwamna Zulum a lokacin, a garin na Auno, ya yi kokarin kare sojojin, inda ya ce akwai sojoji a garin, amma gwamnan ya gwasale shi.

“Ka ma daina cewa akwai sojoji. Saboda babu! Duk kiraye-kirayen da muka rika yi a girke sojoji a nan Auno, ba a ji mu ba.

“Ni ba fada ko jayayya ko fito-na-fito za mu tsaya mu na yi a nan da kai ba. Amma maganar sojoji dai a nan babu. Mun sha yin kira a kafa sansani a nan Auno, saboda Boko Haram sun maida garin wurin da ya fi saukin kai hari, amma na a amshi kukan mu ba.” Cewar Zulum.

“Da an ce karfe 5 na yamma ta yi, sojoji sun datse kofar shiga, sai su bar wurin su ma su shiga Maiduguri, su kyale dandazon matafiya a kan hanya, su na jiran a bude hanya gobe da safe.

“Idan za ka umarci sojojin ka su dawo su kafa sansani a Auno, to ka yi. Idan kuma ba za ka yi ba, to kawai ka fada mana. Mu kuma sai mu san abin da za mu yj, a matsayin mu na gwamnati.

“Don girman Allah ka dubi yawan rayukan da aka rasa a wurin nan. Idan ka na tababa, to ka matsa ka kidaya gawarwaki da kan ka.”

Daga nan Zulum ya nuna takaicin yadda aka yi wannan mummunan hari, tare da cewa, “Jami’an DSS sun kawo rahoton gargadin yiwuwar kawo hari, kamar yadda suka taba bada rahoton na Jakana, amma ba a yi komai a kai ba.

” Ni dai a daina duk wata doguwar magana. Don Allah ku dawo da sojoji, a matso da shingen sojoji a nan Auno. Saboda daga nan zuwa Jami’ar Maiduguri fa kilomita 8 ne kacal. To idan har ba za a iya kare lafiyar jama’a a nan da kuma da Jami’a ba, ai mu da ke cikin Maiduguri ma mu na cikin tashin hankali kenan. Domin abin da ya ci Doma, ba zai kyale Awai ba.” Inji Gwamna Zulum.

Harin Auno: Laifin Matafiya Ne -Babban Kwamandan Yakin Boko Haram

Babban Kwamandan Yaki Da ‘Yan Boko Haram, Olusegun Adeniyi, ya ce matafiya ne da kan su suka haifar da wannan mummunan hari da Boko Haram suka kai musu a Auno, inda suke yada zango su kwana.

Bayan ya nuna jimami, alhini da takaicin kisan, Adeniyi ya ce masu motoci sun ki bin umarnin da sojoji suka yi cewa idan yamma ta yi su kaurace wa titin Damaturu zuwa Maiduguri.

Ya ce mun sha sanarwa cewa idan direba ya san ba zai iya kaiwa ko shiga Maiduguri kafin ko karfe 5 na yamma ba, to kada ma ya kuskura ya biyo titin.

Adeniyi ya ce su na kulle hanyar ce a haka motoci gilmawa da dare domin cikin daren ne sojoji ke sintirin yaki da farautar Boko Haram a yankin.

“Da rana sojoji na aikin tsaron titi da masu tafiya kan titin. Idan dare ya yi kuma ana kulle titin ne saboda sintirin farautar ‘yan ta’adda sojoji ke yi.

“Don haka bai kamata wanda ya san motar sa ba ta da gudun da zai iya shiga Maiduguri ba, ya yi gangancin baro ganin Benisheik ba. Saboda ya san ba zai shiga Maiduguri ba, ba za a bar shi ba, sai dai ya kwana a kan hanya.” Inji Adeniyi.

Buhari Ya Jajanta
Shugaba Muhammadu Buhari ya jajanta a kan mummunan kisa da kone dukiyoyi da Boko Haram suka yi a Auno, a kan matafiya, a ranar Lahadi.

Yayin da ya ke nuna alhini, Buhari ya ce Najeriya ba za ta gajiya ba, wajen ganin an kawo karahen ‘yan ta’adda a kasar nan.

Ya nuna cewa Boko Haram ba su da karfi sosai a yanzu, shi ya sa suke kai harin sar-ka-noke, wato harin-matsorata a kan fararen hula.

Ya sha alwashin magance kalubalen tsaro a kasar nan.

Share.

game da Author