Boko Haram na kai wa Kiristoci hari don su tada rikicin addini – Lai Mohammed

0

Ministan yada Labarai Lai Mohammed ya bayyana cewa hare-haren da Boko Haram suke kaiwa majami’u da wuararen bautan kiristoci ya fara wuce gona da iri, kuma suna yin haka ne don su ingiza mutane a kaure da rikicin addini a Kasar nan.

Lai Mohammed ya kara da cewa duk da ba wai BOKO Haram sun dai na kai wa musulmai hari bane, yanzu sun canja salo, suna bi majamiu da wuraren bautan kiristoci ne suna musu diran kawara. Sai kashe mutane sannan su dagargaza wuraren bautan.

” A dalilin bakar wahala da kokarin darkake su da jami’an tsaron Najeriya suke kokarin yi, Boko Haram sun canja salon hare-haren su. Yanzu sun karkata zuwa far wa kiristoci ne a gidajen su da wuraren bautan su.

” Kuma suna yin haka ne domin kawai su kawo rashin natsuwa a tsakanin musulmai da kiristocin Najeriya, sannan da ingiza wasu a rincabe cikin rikicin addine. Wannan Shine burin su.”

Daga nan sai ya kara da dewa wannan kungiya na Boko Haram zata ci gaba da dandana kudar ta daga da bakar azaba a hannun dakarun Najeriya.

Ya ce jami’an tsaro za su ci gaba da yi musu luguden wuta da hana su sakat a duk inda suke har sai an gama da su.

Share.

game da Author