Mutanen jihar Barno sun kammala azumin kwana daya da gwamnan jihar Babagana Zulum ya yi kira ga da ayi.
Wannan kira da Zulum yayi ranar Juma’a ya samu karbuwa matuka domin hatta daliban makarantun jihar duk sun tashi da azumi ranar Litinin.
” Abin ya bani mamaki matuka ganin yadda daliban ajina duk suka zo makaranta suna azumi.” Haka malamin makaranta ya ce.
Gwamna Zulum ya yi kira ga mutanen jihar da su tashi da azumi sannan a tsananta addu’o’i domin Allah ya kawo karshen Boko Haram a jihar.
” A cikin addu’o’in kada mu manta da ‘yan uwan mu da suka rasu a sanadiyyar hare-haren Boko Haram. Mu saka su cikin addu’o’in.
” Sannan mu ciyar da da wadanda basu da shi, sannan da addu’o’i.
Matsalar tsaro da hare-haren Boko Haram yayi kamari a kasarnan a dan watannin nan. Wannan matsala ya sa har kira ake ta yi ga shugaban kasa da canja shugabannin tsaron kasa.