Shugaba Muhammadu Buhari ya dora laifin yawan farmakin da Boko Haram ke kai wa a Barno a kan shugabannin jihar.
Ya ce al’umma da shugabannin jama’a ba su bayar da hadin kai ga sojoji domin kawo karshen Boko Haram.
Ya ce: “Wadannan masu kawo hari, ‘yan Boko Haram ake kiran su ko ma ‘yan me za a kira su, ba za su iya shigowa cikin Maiduguri ba ko kewayen ta ba tare da sanin shugabannin al’ummar yankin ba.”
Buhari ya fadi haka a lokacin da ya ke na shi bayanin bayan da Gwamna Babagana Zulum da Shehun Barno sun yi masa bayanin halin da ake ciki dangane da maharan.
Buhari ya kai ziyara ce a Maiduguri, mako daya bayan mummunan harin da Boko Haram suka kai wa matafiya a garin Auno, inda suka kashe matafiya 30 tare da kone motocin su da wasu gidaje 18.
An kuma tabbatar da cewa sun arce da wasu matafiya da dama.
An kai harin ne a lokacin da Buhari ke wurin taron Kungiyar Kasashen Afrika, a birnin Addis Ababa na Ethiopia.
An yi ta caccakar sa dangane da yadda rashin tsaro da sauran nau’ukan kashe kashe ke ta ruruwa a fadin kasar nan, musamman a Arewa.
Zuwan Buhari a Maiduguri ya sha mamaki, inda dimbin jama’a da suka yi sahu-sahu a gefen titi suka rika eho da sow ace, “Ba ma yi, ba ma so!”
Hukumar sojojin Najeriya ita ma ta dora kisan da aka yi wa matafiya a kan su matafiyan, abin da bai yi wa jama’a da dama dadi ba a kasar nan.
A Maiduguri, Buhari ya ziyarci fadar Shehun Barno, inda ya yi ta’aziyyar wadanda Boko Haram suka yi wa mummunan kisa a Auno.
Ya roki Buhari ya kara maida hankali wajen tsaro.
Umar Garbai ya ce wa Buhari a baya an samu saukin Boko Haram sosai, amma a yanzu abin ya yi muni matuka.
A nasa bayanin, Zulum ya ce an samu nasarar Boko Haram sosai daga 2015 har zuwa Fabrairu 2019.
Ya ce daga watan Maris 2019 ne aka rika samun hare-haren da Boko Haram suka rika kaiwa babu kakkautawa.
Daga nan sai ya yi kira ga sojojin Najeriya su kara zage damtse ta hanyar kara nuna azamar samun irin nasarar da suka samu kan Boko Haram, tsakanin 2016 da 2017.
“Muna so mu ga sojoji na nausawa sun a kai wa Boko Haram hari har a cikin Dajin Sambisa. Mu na so mu gas u na dannawa a a bakin Tafkin Chadi sun a kakkabe ‘yan Boko Haram.”
Buhari Bai Je Auno, Inda Boko Haram Suka Banka Wa Matafiya Wuta Ba
Sai dai kuma duk da kai ziyarar jaje da ta’aziyya a Maiduguri, Buhari bai je Auno ba, inda Boko Haram suka banka wa mafiya wuta.
PREMIUM TIMES ta tabbatar da cewa mazauna garin Auno sun jera bakin titi, su na jiran tsammanin Buhari zai karasa a garin.
Sai dai Buhari bai kai ziyarar gane wa idon sa dimbin motocin da aka kona ba.
Tsakanin Auno da Filin jirgin Maiduguri kilomita 15 ne, inda a kasa da minti 20 za a iya karasawa garin.