BOKO HARAM: Bayan agajin naira bilyan 122.5, Amurka za ta kara wa Najeriya naira bilyan 14

0

Amurka ta yi wa Najeriya alkawarin kara mata agajin dala milyan 40 a wannan shekarar, kwatankwacin naira bilyan 14, domin shawo kan mummunan halin da dimbin ‘yan gudun hijira ke ciki a kasar nan.

Wannan ba ya cikin lissafin kayayyaki, agaji, ayyuka da kudaden da Amurka da dumbuza wa Najeriya a cikin 2019, har dala milyan 350 domin shawo kan masu gudun hijira da dakile ta’addanci.

Dala milyan 350 na dai-dai da naira bilyan 122.5. Su ne Najeriya ta samu na kayan agaji da kudade daga Amurka a shekarar da ta gabata.

Alkawarin kara bayar da wannan agaji ya fito ne daga bakin Sakataren Harkokin Kasashen Waje na Amurka, Mike Pompeo, a lokacin da ya ke taron ganawa da Ministan Harkokin Waje na Najeriya, Jeffrey Onyeama.

Sun yi wannan ganawar a birnin Washigton, babban babban birnin kasar Amurka.

“Ina sane da halin da Najeriya ke ciki dangane da matsalar tsaro. Abin ya na damun mu sosai. Shi ya sa ma Amurka ta amince ta kara wa Najeriya tallafin kayan agaji da sauran abin da ya saukaka, har na dala milyan 40.

” Babban abin damuwa shi ne halin da masu gudun hijira suka tsinci kan su, saboda rashin tsaro. Shi ya sa a baya ba mu yi kasa a guiwa ba wajen bayar da gudummawar kaya da ayyukan agaji da kudade kimanin jimlar dala milyan 350.”

Wannan ganawa ce musamman ta tuntubar juna dangane da batutuwa, musamman da suka tsafi tsaro a kan Kasashen biyu.

Minista Onyeama ya kara da cewa sun kuma tattauna batun jiragen yakin nan 12 da tuni aka biya wani kamfanin Amurka kudi domin ya kera Najeriya da za a yi amfani da su wajen yin wa Boko Haram rubdugun-bai-daya, yadda za a kawo karshen shekaru 10 da a ke yi wajen yaki da Boko Haram.

Najeriya ta biya Amurka zunzurutun dala miliyan 500 domin a samar mata jiragen, tare kuma da bayar da horo kwarewa ga matukan jiragen da wadanda za au rika yaki da shi.

Pompeo ya ce jirage ne na zamani wadanda ko kadan ba a tabatar irin barnar da za su rika yi wa Boko Haram.

Jiragen 12 dai samfuran A-29 ne da ake ta dakon jiran kawo su tuni.

Sama da shekaru 10 kenan Najeriya, Chadi, Nijar da Kamaru na fama da Boko Haram.

Daga makonni biyu zuwa yau, Majalisar Tarayya da sauran jama’a da dama na ta yin kiraye-kirayen a tsige shugabannin tsaron kasar nan, ganin yadda matsalar tsaro ke kara dagulewa.

Akwai dubban daruruwan ‘yan gudun hijira a Jihar Barno da wasu garuruwa. Wasu da dama sun tsallake zuwa Chadi da Kamaru da Jamhuriyar Nijar.

Sai dai kuma Sakataren Amurka ya yi gargadin cewa kada a yi amfani da jiragen wajen adka wa wadanda ba su ji ba, ba su gani ba. Ya kuma yi tsokaci a kan damuwar take hakkin jama’a da ake korafi na faruwa a Najeriya.

A kan haka ne Minista Onyeama ya shaida masa cewa ‘yaki da ta’addanci a Najeriya ba sabon abu ba ne, ya kai shekara 10. Don haka Najeriya na bakin kokarin ta wajen kauce wa daga take hakkin jama’a.

Idan ba a manta ba, cikin 2016 wani jirgin yakin Najeriya ya jefa bam ya kashe daruruwan masu gudun hijira a bisa kurkure, a garin Rann, jihar Barno.

Share.

game da Author