BIYAYYAN UBANGIDA: Buratai ya diran wa Monguno, ya fallo na sa takobin

0

Da alama dai shima babban hafsan sojojin kasan Najeriya  Tukur Buratai ya na tare ne da shugaban ma’aikatan fadar shugaban Kasa Abba Kyari a cakwakiyar da ta sarkake shi da maiba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaron kasa, Babagana Monguno.

Domin a rage wa ofishin NSA wato Monguno karfin iko da karfin tsiya, a cikin wannan watan, Buratai ya kakkabe dukka sojojin dake aiki tare da shi Monguno a ofishin sa. Buratai ya umarci da a janye su duka sannan bai musayansu da wasu ba.

Kwanaki kadan bayan an umarci wasu manyan sojoji masu mukamin Kanal bakwai da janar Janar uku dake aiki a ofishin NSA  su gaggauta komawa bariki sannan ba a turo wasu a madadin su domin maye gurbin su ba, ranar 4 ga watan Fabrairu sauran manyan sojoji 13 da ke aiki a NSA din suma aka umarce su su dakatar da zuwa aiki a wannan ofishi na NSA. Hakan yasa kenan an bar bangaren ofishin ONSA babu tsaro na soja kwata-kwata.

Manyan sojoji 23 kenan aka dage daga ofishin ONSA ba tare da an musanya su da wasu ba. Dukkan su  a ranakun 4 da 10 ga watan Fabrairu.

Ko da yake shi Monguna baya kasan a lokacin da Buratai ya rika yin wadannan canje canje a ofishin sa dawowarsa ke da wuya sai ya umarci duka wadanda Buratai ya canja wa wajen aiki su koma bakin aikin su a ONSA din, yana mai cewa kada su bi umarnin sa.

Amma har yanzu Buratai bai ce komai ba game da haka kuma bai canja shawarar sa ba kuma bai ce komai ba game da umarnin Monguno ga sojojin da ya janye daga ofishin ONSA din.

Buratai ya amince da takardar canjin wasu manyan sojoji 137 dake aiki a wurare dabam dabam na ma’aikatu da sansanoni, bariki da sauran su na sojoji a tsakanin ranakun 4 da 10 na watan Fabrairu. Sannan aka janye nanyan sojoji 23 gaba dayan su ba tare da an musanya su da wasu ba a ofishin NSA wanda ba a taba yin irin haka ba.

‘Wadanda abin ya shafa sun hada da Manjo-Janar Adeyinka Famadewa wanda shine shugaban ma’aikatan ofishin NSA,  da kuma Kanal Ado Ibrahim da shima mai taimakawa wa Monguno a ofishin NSA ne. Shi an maida shi Jaji, jihar Kaduna.

Wannan ofis na mai ba shugaban kasa shawara kan harkar tsaro na da tulin ma’aikata a dalilin irin nauyin da ke kan ta na maganan tsaron kasa.

Jami’an ‘Yan sanda, Sojin Sama, Kasa da na Ruwa, Hukumar Tsaro na Sirri, EFCC, Sibul Difens, Kwastam, Shige da fice duk suna da jami’ai da ke aiki a karkashin ofishin NSA.

Sai dai wani tsohon ma’aikacin NSA da ya zanta da PREMIUM TIMES cikin sirri ya bayyana cewa kowacce hukuma ko ma’aikata da ke aiki a NSA za ta iya canja jami’anta a duk lokacin da ta ga dama, ” Sai dai kuma dole sai an sanar da NSA kafin a yi wannan canji saboda akwai matakai masu tsauri da ake bi kafin a yarda ka yi aiki a ofishin NSA. Don haka ba haka kawai za ya janye ma’aikaci ba ko kuma a musa ya ma’aikacin da ke aiki a ofishin NSA.

Dukkan wadanda aka janye su daga ofishin NSA, an umarce su da su gaggauta komawa wuraren da aka tura su cikin kwana uku ko su fuskanci horo.

Shi dai Monguno ya kafe kan babu wanda zai tafi da ga cikin duka sojojin da Buratai ya janye su daga ofishin sa, yana mai cewa wannan abu da Buratai yayi, nuni ne kawai na nuna goyon baya ga Abba Kyari wanda shine gogarman da ke karewa da tsare musu kujerunsu  kada Buhari ya fatattake su duk da ‘yan Najeriya sun ce sun gaza, wato Buratai da sauran manyan hafsoshin rundunonin sojin Najeriya.

Masana harkar tsaro da suka tattauna  da wannan jarida sun shaida cewa akwai hadarin gaske kan abinda yake faruwa a tsakanin Abba Kyar da Monguno domin duka ya shafi tsaron kasa.

Sun nuna cewa bai kamata Buhari yayi burus, ya tsuke bakin sa ya yi shuru  bayan ga gobara nan na su ta tashi a karkashinsa tsakanin manyan makusantan sa biyu.

Dole fa ya gaggauta taka musu birki, a samu mafita tun da wuri.

” Babu inda dokar kasa ta ba hadimin shugaban kasa daman da zai rika yin katsalandan a harkokin tsaron kasa, har ya kai ga yana neman ya yi sa-in-sa da ofishin NSA.  Lallai akwai abin dubawa a nan kuma cikin gaggawa.”

  

Share.

game da Author