BIDIYON TSIRAICI: Maryam Booth ta yi barazanar maka tsohon Saurayinta Kotu

0

Fitacciyar ‘yar wasan fina-finan Hausa, Kannywood, Maryam Booth ta yi barazanar maka tsohon saurayinta a kotu a dalilin sakin wani bidiyon ta na tsarsici.

Maryam ta bayyana haka ne a doguwar sako da ta saka a shafinta ta Instagram inda ta ce ta maida wa tsohon saurayin nata martani ne bayan sakon nisanta kansa da yayi da wannan bidiyo sannan ya saka a shafin sa ta Instagram.

Idan ba a manta ba, a makon da ya gabata ne aka saki wani bidiyo dake nuna jarumar tsirara a daki tana kokarin canja kayan sawa.

Wannan bidiyo ya karade shafukan soshiyal midiya.

Maryam ta ce tana nazarin abinda ya faru, tana mai cewa abin ya kai shekara uku da aukuwa.

” Wannan bidiyo ya kai shekara uku da daukar sa kuma na san wanda ya dauka. Tun bayan daukar bidiyon aka rika yi min barazanar sai an saki bidiyon. Na yi kokarin ganin bai kai ga an sake shi tun a wancan lokaci.

” Lallai da gaske ne, Mawaki Deezell, Ibrahim Rufai tsohon saurayina ne, kuma shine ya dauki wannan bidiyo a boye a lokacin da nake canja kayan sawa.

” Ko ma dai wanene ya fitar da wannan bidiyo zai dandana kudar sa domin a yanzu haka ina tattaunawa da lauyoyi na domin daukar mataki akai.

Amsar Deezell

Deezell, ya karyata korafi da zargin Maryam Booth a sako da ya fitar bayan ya karanta zargin da aka yi masa.

Deezell ya ce ba shi da masaniya game da wanda ya saki Bidiyon. Sannan ya ce shima ba zai maganar ta mutu batare da ya bi hakkin sa ba.

” I dan ya kai ga in garzaya kotu ne zan garzaya domin ban san abinda ake fadi ba. Ban taba sakin wani bidiyo irin haka ba.

Jaruman Kannywood sun fito sun nuna goyon bayan su ga Maryam Booth sannan sun roke ta da ta kwantar da hankinta ta ci gaba da yin taka-tsantsan akan abin.

Share.

game da Author