Bayan watanni shida, har yanzu babu labarin Dadiyata

0

Watanni shida kenan cif-cif tun bayan shigar-kutsen da wasu da suka rufe fuskokin su cikin gidan sa, suka arce da shi da karfin-tsiya, har yau an rasa inda Abubakar Idris, wanda aka fi sani da Dadiyata ya ke.

Bayan da mahara suka ritsa shi a gida karfe 1:00 na dare, a daidai lokacin da ya ke fita daga motar sa, sun maida shi cikin motar, suka arce da shi, kuma har yau ba a san halin da ya ke ciki ba.

Bisa dukkan alamu wadanda suka sace shi, su na biye da shi ne. Sun afka cikin gidan daidai lokacin da ya ke shiga da motar sa a gidan. Suka nuna masa bindiga, suke fice da shi a motar sa, kirar BMW.

Dadiyata, ya kasance mai sharhi a soshiyal midiya, kuma rikakken mai adawa ne da caccakar salon mulki da siyasar Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje.

Har zaben 2015, Dadiyata rikakken mai adawa ne da salon mulkin tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan.

Bayan an gudu da Dadiyata lokaci mai tsawo babu labari, an yi tunanin jami’an SSS ne suka yi shigar-burtu, suka yi masa kamun-dare.

Wannan ya sa matar sa Hannefa Idris ta maka Rundunar SSS ta Kaduna, ‘Yan Sanda, Gwamnatin Jihar Kaduna kotu, inda ta nemi a gaggauta sakin mijin ta ba da wasu sharudda ba. Ta kuma nemi a biya diyyar naira milyan 50.

Dukkan wadanda aka maka kotun dai sun musanta hannu a kama su, kamar yadda SSS suka ce ba su je sun kama shi ba.

Ganin yadda jami’an tsaro suka nesanta daga kama shi, duk kuma da cewa akwai wadanda ba su gamsu ba, yanzu kuma tambaya ake ta yi shin ina Dadiyata ne?

Matar sa ta shaida wa PREMIUM TIMES a ranar Lahadi cewa har yau karar da ta shigar na kotu, a gaban Mai Shari’a.

Sannan ta ce rabon da ‘yan sanda su tuntube ta, an dade sosai.

PREMIUM TIMES ta tuntubi Kakakin Yada Labarai na Rundunar ‘Yan Sandan Kaduna, Yakubu Sabo a ranar Litinin. Ya ce su na ci gaba da bincike iyakar iyawar su, amma har yanzu babu wata alamar inda za a gano shi.

“Mun bi hanyoyi daban-daban na bincike, har da amfani da na’ura, amma mun kasa warware yadda za mu gano shi. Mu na kan bincike.”

Idan za iya tunawa, Dadiyata ya taka rawa a soshiyal midiya, wajen yaki da kamfen din kayar da PDP a zaben 2015.

Bayan an kafa mulki kuma bambancin tafiyar siyasa ya sa Dadiyata ya tsaya cikin Kwankwasiyya, ya raba hanya da Gwamna Ganduje, ya rika caccakar gwamnan.

Har zuwa lokacin da aka sace Dadiyata, ya na zaune da iyalan sa a Kaduna, amma ya na koyarwa ne a Jami’ar Gwamnatin Tarayya ta Dutsinma, Jihar Katsina.

Share.

game da Author