BAYAN HARIN GARKIDA: Zan yi wa Boko Haram kwaf-daya -Inji Buhari

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya kara jaddada abin da ya kira gagarimin shirin da ya ce gwamnatin sa ta yi, domin tasar wa Boko Haram gadan-gadan, a yi musu kwaf-daya, a wuce wurin.

Buhari ya yi wannan bayani ne a cikin kalaman alhini ga al’ummar garin Garkida, inda Boko Haram suka kai hari ranar Juma’a da dare, a Jihar Adamawa.

Kakakin Yada Labarai Garba Shehu ne ya sanar da wannan jimami ga al’ummar Garkida.

Da ya ke jajantawa, Buhari ya ce gwamnatin sa na ci gaba da yin galaba a kan Boko Haram. Ya ce hare-haren sari-ka-noke da Boko Haram ke kai wa a wasu yankuna, hakan ya na nuna cewa an karya musu fuka-fiki, ba su iya dogon zangon kai hare-hare.

Wata nasarar da Buhari ya ce an samu ita ce, a yanzu Boko Haram ba su rike da kowane yankin na kasar nan.

Ya ce Boko Haram sun maida hankali yanzu a wasu wuraren da babu tsattsauran tsaro, su na kai farmaki.

Sau ya yi kira ga jami’an tsaro da su tabbatar sun rika bin Boko Boko Haram su na ganawa da su a wuraren da su ke guduwa su na boyewa.

Daga nan kuma ya jinjina wa sojojin da suka yi arangama da Boko Haram.

PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda Rundunar Bataliyar Sojoji ta 232 ta ce sojojin ta na Burged ta 23 da ke yakin ‘Operation Lafiya Dole’, wadanda aka girke a Gombi, sun tarwatssa gungun Boko Haram da suka yi kokarin kai hari a garin Garkida, Karamar Hukumar Gombi, cikin Jihar Adamawa.

Mataimakin Daraktan Yada Labarai na Runduna ta 23, Haruna Sani ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar.

Sai dai kuma a cikin sanarwar ya ce maharan sun dira a wani gari, inda suka rika banka wa gine-gine wuta kuma su na harbe-harbe.

Ya ce daga nan fa sojoji suka tunkare su aka rika bude musu wuta.

Ya ce maharan sun isa garin a cikin motocin harba manyan bindigogi da kuma wasu a kan babura.

Ya ce an kashe Boko Haram da dama, wasu kuma an ji musu raunuka,. Daga nan suka tarwatse, suka tsere, yawanci da raunuka a jikin su, kamar yadda aka rika ganin zubar jini a hanyar da suka bi suka arce.

Amma kuma ya ce soja daya ya rasa ran sa, daya kuma an ji masa ciwo.

Ya ce Kwamandan Burget ta 23, Sani Mohammed ya ziyarci garin na Garkida, kuma ya je ya ga irin abin da iya faru a garin.

Kwamandan ya jinjina wa sojoji da jama’ar garin.

Yadda Rahotanni Suka Bayyana Barnar Boko Haram a Garkida

Kafafen yada labarai da dama, ciki har da Punch da Sahara Reporters, sun buga bayanai da hotunan iron barnar da Boko Haram ta yi a garin Garkida, wanda mafiya rinjayen al’ummar garin Kiristoci ne.

Cikin wuraren da da suka banka wa wuta, har da babban asibitin garin, wato Garkida General Hospital.

Rahotanni daga wasu kafafen yada labarai sun ruwaito cewa Boko Haram sun kone barikin ‘yan sanda, Ofishin ‘Yan Sanda coci-coci guda biyu da kuma gidan wani tsohon Janar na mai ritaya, wato Paul Tarfa.

Kungiyar ta’addancin ISWAP ta ce ita ce ta kai harin. Ta kara da cewa ta kashe soja uku, ta arce da wasu masu bauta da ta ritsa a cikin coci.

Coci-cocin da aka kone sun hada da Living Faith da kuma EYN. Sun nuna cewa sun yi awon gaba da wasu mutane da suka kama a kauyukan da suka keta.

Garkida na yankin Gombi kan hanyar Gombi zuwa Biyu zuwa Damaturu.

Share.

game da Author