Tsohon Shugaban Hukumar EFCC na farkon kafa ta, Nuhu Ribadu ya karyata da kakkausar murya wasu bayanai na kage, sharri da karya da tuggu da ake yadawa a soshiyal midiya cewa wai ya taba Shugaba Muhammadu Buhari da Gwamna Nasir El-Rufai na Kaduna su ne masu daukar nauyin ‘yan bindigar Arewa.
Ya ce karairayi aka kitsa da shaidancin bata suna, inda ake yada cewa wai ya taba cewa, “su Buhari, El-Rufai da Dambazzau ne suka kirkiro ‘yan bindiga a Arewa, domin kawai su yi amfani da su wajen wancakalar da shugaban lokacin, Goodluck Jonathan daga mulki.”
Haka dai rahoton da ake yadawa din ya nuna, wanda tuni Ribadu ya ce kage da sharri da kuma shaidancin wasu shaidanu ne da kuma annamimai.
Tare da nesanta kan sa daga wannan karairayi, Ribadu ya yi kira ga jami’an tsaro su gaggauta bankado wanda ko wadanda suka kitsa wannan sharri su ke yadawa a soshiyal midiya.
Ya roki jama’a da cewa duk wanda ya ci karo da wannan shirme, sharri da shirbitsin shiririta a soshiyal midiya, to ba rubutu ko furucin shi Ribadu din ba ne.
Ribadu da jigo ne yanzu a jam’iyyar APC ya karyata wannan labari da ake ta yadawa cewa sharri mahassada ne.