Majalisar Dokokin Jihar Zamfara ta kafa kwamitin mambobi bakwai da su binciki yadda gwamnatin tsaohon gwamna Abdulaziz Yari ta bayar kwangilar gina sabon Gidan Gwamnati a kam kudi naira biliyan biyu.
Kakakin Majalisar Jihar, Nasiru Magarya ne ya yi wannan sanarwa cewa Majalisar Zamfara za ta binciki yadda aka yi da wannan kwangila ta naira bilyan biyu.
An amince da kafa wannan kwamiti ne bayan da Danmajalisar mai wakiltar Maradun-1, Honarabul Dosara ya gabatar da neman a yi wannan bincike.
Dosara ya ce akwai hujjojin alkaluman kudade da ke nuna cewa gwamnatin da ta shude kafin ta Gwamna Matawalle a bayar da kwangilar gina gidan gwamnati a kan kudi naira bilyan biyu.
Ya ce akwai bukatar majalisa ta binciki yadda aka yi da kudaden da kuma batun kwangilar.
Mataimakin Kakakin Majalisa, Musa Bawa da Kabiru Magaji, dukkan su ’yan PDP, suka yi kira da a kafa kwamitin bincike.
Kakakin Majalisa ya ce an bai wa kwamitin da aka kafa kwata daya domin ya yi bincike kuma ya gabatar wa majalisa da rahoton da ya binciko.
Musa Bawa wanda shi ne Mataimakin Shugaban Majalisa ne aka nada shugaban kwamiti, Sai Shugaban Masu Rinjaye, Faruk Dosara, Zaharadden Sada, Ibrahim Na’idda a matsayin mambobi.
Sauran mambobin sun hada da Yusuf Alhassan, Salisu Usman da Masur Daki Takwas.
Tun bayan saukar tsohon gwamna Abdulaziz Yari, ya ke fama da shan bincike iri daban-daban.