Karamin Ministan kiwon lafiya Olorunnimbe Mamora ya bayyana cewa babu tabbacin maganin Chloroquine na warkar da cutar Coronavirus.
Mamora ya fadi haka ne a taron bayyana matakan da gwamnati ta dauka domin hana shigowar cutar a kasar nan.
Ya ce kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta hada hannu da kwararrun likitoci domin gano maganin kawar da cutar.
” WHO da R&D Blueprint sun fara gudanar da bincke kan gano magungunan cutar kanjamau guda biyu da Remdisivir da Lopinavir da Ritonavir domin ganin ko suna da ingancin kawar da Coronavirus. Sannan maganin Chloroquine itace magani na uku da suke gudanar da bincke a kai.
Mamora ya wayar da kan mutane ne domin kawar da rade -radin da ya game gari cewa maganin Chloroquine na warkar da cutar coronavirus.
“Har yanzu babu maganin cutar amma ana yin bincike sannan har yanzu cutar bai shigo Najeriya ba.
Ya kuma ce gwamnati ta yi kyakkyawar tanadi wajen ganin cutar bata shigo kasar nan.
” Mun bude wuraren gwajin cutar a jihohi Edo da Legas da babban birnin tarayya Abuja.
” Sannan mun karfafa matakan hana yaduwar cutar a tashoshin jiragen sama da ruwa.
Bayan haka babban sakataren ma’aikatan kiwon lafiya Abdulaziz Abdullahi, ya ce gwamnati ta bada Naira miliyan 386 domin inganta aiyukkan hana shigowa da cutar a kasar nan.
Abdullahi ya ce wannan kudade na cikin Naira miliyan 620 da gwamnati ta ware domin dakile yaduwar cutar.
Ya ce za a raba wadannan kudade ne tsakanin hukumar hana yaduwar cututtuka ta kasa (NCDC) da Hukumomin kiwon Lafiya dake tashoshin jiragen sama da ruwa.