Ministan Sadarwa, Ali Pantami ya bayyana cewa ba zai iya cewa komai ba game da harajin da ka kara a kudin kira na wayan selula.
Minista Pantami ya ce maganan karin haraji ba ya karkashin ofishin sa.
” Ma’aikatar sadarwa bata da ikon kara kudin katin kira ko saka haraji a kira. Hakan yana karkashin hukumar tara haraji ta kasa ce.
Ya roki masu korafi a kawai da u garzaya hukumar tara haraji ta kasa wato FIRS domin mika kukan su.
‘Yan Najeriya na kokawa game da karin haraji da gwamnati ta yi akan kudin kira a wayan selula a kasar nan.
Sai dai kuma ma,’aikatan a cikin wannan makon ya kafa sabbin sharuddan mallakar layi a kasar nan.
Ga sharuddan
1. A rika yin rajista bisa Dokar Sadarwa ta 2003, mai lamba 25, Sashe na 25.
2. Duk wanda zai yi rajistar sabon layi, tilas sai ya bada lambar Shaidar Katin dan Kasa (NIN).
3. Duk wani dan kasar waje da ya shigo Najeriya, idan zai mallaki layin waya, tilas sai ya hada da lambar fasfo da ta biza din sa.
4. Sai nan da ranar 1 Ga Disamba za a kulle uzurin rashin yin wannan rajista.
5. Ba a yarda mutum daya yya mallaki layukan waya fiye da uku ba.
6. Duk lambar da jami’an tsaro suka tabbatar da an taba aikata laifi da ita, to za a kulle ta.