Babban Bankin Najeriya (CBN), ya karyata rahoton da wata jarida ta bugs, inda aka ce ya kai manoman da suka karbi lamunin kudin noma daga CBN kotu, saboda kin biyan bashin da suka karba.
Kakakin Yada Labarai na CBN, Isaac Okorafor, ya bayyana cewa wannan rahoton ba gaskiya ba ne.
Jaridar Daily Trust ta buga labarin cewa Shugaban Kungiyar Manoman Shinkafa na Jihar Kebbi, Muhammed Augie, ya ce har yau wadanda suka karbi bashin CBN tun a cikin 2015, su 70,000 ba su biya bashin ba.
An ruwaito Augie ya na cewa manoma 200 ne kacal daga cikin 70,000 wadanda suka karbi lamunin suka biya na su a Jihar Kebbi.
Augie ya kara da cewa, kafin a bayar da lamunin ana nima metirik tan 70,000 na shinkafa, amma bayan karbar lamunin na naira bilyan 17, an rika noma har metirik tan din shinkafa milyan 1.6.
“Duk da haka amma karbo bashin ya zama jekala-jekala. Sai da mu ka hada kotuna. Yanzu duk kotunan Majistare da ke a Kebbi za ka ga mun maka manoman da suka ji biyan kudin a can. Har yau mutum 200 kadai ya biya bashin.” Inji Augie.
Sai dai Okorafor na CBN ya ce naira bilyan 16 ne aka raba a Jihar Kebbi, ba bilyan 17 ba. Kuma duk an karbi kudaden, sauran da ba a kai ga karba ba, naira bilyan 2.6 ne suka rage a hannun manoma.
Ya kuma yi karin hasken cewa maimakon a kai manoma kotu domin su biya kudaden, sai aka amince CBN ta kara wa manoman wa’adin lokacin biyan basussukan.
Sai dai wani da ba ya son a bayyana sunan sa, ya karyata Okorafor, domin ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa an kai manoma da yawa kotu, kuma su na ta kokarin ganin sun biya.
“Ai su a zaton su kudin ko sun cinye babu wani abin da za a yi musu.” Inji majiyar mu.
Discussion about this post