Babban Limamin Darikar Katolika na Sokoto, Bishop Mathew Kukah, ya yi wa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ragargazar da bai taba yi mata ba.
Ya ce tun da aka kafa Najeriya ba a taba yin gwamnati da ta nuna kabilanci, bangaranci da ninanci a fili karara kamar ta Buhari ba.
Hassan Kukah ya yi wannan ragargaza a wurin jana’izar rufe gawar wani matashin mai koyon ayyukan wa’azi da sakonnin bushara, mai suna Michael Nnadi da masu garkuwa suka kashe, a Jihar Kaduna.
An kama Micheal tare da abokan kararun sa uku, Pius, Peter da kuma Stephen. Sun saki ukun, amma suka ci gaba da tsare Michael Nnadi tsawon makonni uku.
Daga baya sun kira wayar kakar sa Nwokwocha, suka shaida mata wurin da za ta je ta dauko gawar jikan ta mai shekaru 18, tare da ce masa sun kashe shi.
Kukah ya fara tuna irin alkawurran da ya ce Buhari ya dauka kafin a zabe shi a shekarar 2015, a wani jawabi da ya gabatar a Cibiyar Inganta Dimokradiyya da Nagartar Gwamnati ta Chatham House da ke birnin Landan.
“Idan na tuna irin alkawurran da Shugaba Buhari ya yi a Chatham House kafin a zabe shi, sannan kuma na kalli abin da ke faruwa a halin yanzu, sai kawai na lullube jiki na da mayafin da-na-sani.
” A wurin ne Buhari ya yi wa duniya alkawarin cewa idan aka zabe shi, zai inganta tsarin aikin soja, zai bi diddigin salsalar bullar ta’addanci tare da magance matsalar tun ma daga tushen ta.
“Sannan kuma ya yi alkawarin shigo da tsare-tsaren inganta tsaro ta yadda zai dakile da hana yaduwar matsalar tsaro a sauran sassan kasar nan.
” Amma a yanzu fa, babu wanda ya taba tunani ko hasashen cewa Buhari assasa kabilanci, bangaranci da ninanci a aikin soja da sauran bangarorin tsaron kasar nan.
“To babban abin haushi da takaicin ma shi ne yadda fifita wani bangare ko kabilancin na bai tsinana komai wajen kawar da milyoyin kananan yaran da ke gararamba a kan titinan garuruwan Arewa ba.
“A yau Arewa ce cibiyar katutun kuncin talauci, fatara, zaman-banza, rashin tsaro, kazantar muhalli da dimbin fakirai da musakai.
” Mu na gani Arewa ta koma kango, ta zama katafaren filayen kaburbura, katon tsaunin tsibin kasusuwan matattu, wulakantaccen yankin da keta da mugunta suka yi wa karatu.
“Wadannan matsaloli sun kafa muni saboda mun dade tsawon shekaru ana yaudarar kai da karyar kishi, tsantsar munaficci, karyar nagarta, karyar takawa da imani, karyar kaunar-juna, rashin kunya, rashin mutunci, harkalla da harankazama.”
Da ya koma kan kashe-kashe da ake yi a Arewa, Kukah ya ce karya ce da kuma yaudarar kai a CE wai Boko Haram da sauran ta’adda wai babu alaka da addini.
“Idan za a kama Musulmi da Kirista, a ware Kirista, a saki Musulmi, ko kuma a tilasta wa Kirista shiga wani addini, sai a ce babu batun addinanci a cikin lamarin?
“Ko kuwa don ‘yan ta’adda na kashe har da Musulmi, sai a ce idan sun kashe Kiristoci kada su nuna damuwa? Shin idan dan ka ya yi min sata, kuma ya yi maka sata, don na yi magana sai ka ce ai kai ma ya na yi maka sata?
Kukah ya ce gaba da nuna damuwa kan halin tabarbarwar tsaro a kasar nan, musamman Arewa da ce tun yankin ya na karkarwar rashin lafiya, ta kai ya na jijjiga, to yanzu ta kai Arewa hajijiya ta ke yi, kuma idan babu abin da za ta dafa don ta samu ta tsaya, to fa babu abin da zai hana ta faduwa kasa.
A karshe ya yi kira ga Kiristoci su yafe wa ‘yan ta’adda masu karkaahe su. Maimakon su kullace su, su yi musu addu’ar samun shiriya ta hanyar yi musu wa’azin tsira zuwa shiga ddinin su.