Rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa ta sanar cewa an sako babban sakataren ma’aikatar aiyukka na jihar Jibril Giza.
Kwamishinan ‘yan sanda Bola Longe ya sanar da haka yayin da yake gabatar da wasu batagari 35 a gaban manema labarai da rundunar ta kama ranar Laraba a Lafia.
Ya ce an sako Giza ranar 18 ga watan Fabrairu da misalin karfe 8 na dare.
Longe yace ‘yan sanda sun tsinci Giza ne a kauyen Duduguru dake karamar hukumar Obi bayan wadanda suka yi garkuwa da shi sun arce sun rabu dashi a daji a lokacin da ‘yan sanda suka fafuresu.
Ya kuma karyata rade-radin da ake yi cewa wai sai da aka biya kudin fansa kafin aka sako shi.
Bayan haka longe ya ce rundunar ta yi nasarar kama mutane 12 da ake zargin suna da hannu a yin garkuwa da Giza.
Idan ba a manta ba a wannan mako ne PREMIUM TIMES ta bada labarin yadda wasu masu garkuwa da mutane suka arce da sakatare Giza.
Maharan sun sace Giza ne a gidan sa dake Shabu da karfe 12 na dare ranar 16 ga watan Fabrairu.
Kwamishinan ‘yan sanda Longe ya ce rundunar ‘yan sanda ba za ta yi kasa-kasa ba har sai ta kamo wadannan mutane da kuma ta ceto Giza.
Discussion about this post