Atiku ya roki Trump ya janye dokar hana ‘yan Najeriya shiga Amurka

0

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar ya roki Shugaban Amurka Donald Trump ya sake tunani, ya janye dokar da ya kakaba wa ‘yan Najeriya shiga shiga Amurka.

Atiku ya yi wannan kira ne bayan da Amurka ta yi sanarwar karshe ta cewa ta hana ‘yan wasu kasashe shiga Najeriya har su nemi zama ‘yan kasa a can, ciki kuwa har da Najeriya.

Dokar dai za ta fara aiki daga ranar 21 Ga Fabrairu, kuma cikin kasashen da aka kara daga cikin sunayen da aka haramta, har da Najeriya.

Atiku ya ce duk da dai Najeriya ta yi sakacin kin yi wa Amurka cikakken bayanin ci gaban da aka samu a yaki da ta’addanci da sauran manyan laifuka, ya kamata Trump ya tuna irin dadadden zumuci da dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu, wadda ya ce ta fi ta dukkan sauran kasashe masu tasowa muhimmanci.

Ya kuma tuna wa Trump irin rawar da Najeriya ta taka wajen gudummawar dakarun taron dangi a lokacin Yakin Gabas ta Tsakiya, inda aka kwato kasar Kuwait daga mamayar da Iraqi ta yi mata, tsakanin 1990 zuwa 1991.
Sai kuma gudummawar Najeriya wajen samar da zaman lafiya a kasar Laberiya.

Akalla a shekara ana samun ‘yan Najeriya 22,000 masu shiga Amurka, yawancin su kuma su na neman mafaka ko zama ‘yan kasa a can.

Share.

game da Author