Rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa ta bayyana cewa wasu ‘yan bindiga sun arce da babban sakataren ma’aikatan aiyukka na jihar Nasarawa, Jibirin Giza.
Kwamishinan ‘yan sanda Bola Longe ya sanar da haka wa Kamfanin dillancin labaran Najeriya ranar Lahadi a Lafia.
Longe yace an sace Giza a gidan sa dake Shabu da misalin karfe 12:40 na daren Lahadi.
Ya ce har yanzu dai wadannan mutane basu nemi iyalinsa ba ko kuma su bukaci a biyasu kudin fansa ba.
Longe ya kara da cewa rundunar ‘yan sanda ba za ta yi kasa-kasa ba har sai ta kamo wadannan mutane da kuma ta ceto sakatare Giza.
Idan ba a manta ba a makon da ya gabata ne rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja ta ceto wasu mutane hudu da aka yi garkuwa da su a maboyar masu garkuwa a Abuja.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Abuja, Anjuguri Manzah ya sanar da haka inda ya kara da cewa sun gano maboyar wadannan mahara ne a tsaunukan Sauni dake tsakanin Abuja da jihar Neja yayin da dakarun ‘yan sandan ke farautar su a wadannan tsaunuka.
Discussion about this post